Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Masarautun Jihar biyar karin alawus-alawus da suke samu duk wata.
Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ne ya sanar da haka a cikin bayanan da ya saba yi bayan taron Majalisar Zartarwa ta jihar.
- HOTUNA: Ziyarar Sarkin Kano kasuwar waya inda Bene ya fado
- HOTUNA: Ziyarar Sarkin Kano Da Na Bichi Ga Sarkin Musulmi
A cewar Kwamishinan, a yanzu masaurtar Kano za ta rika samun Naira Miliyan 100 duk wata, yayin da sauran masarautun hudu da suka hada Karaye da Bichi da Rano da kuma Gaya, za su rika karbar Naira miliyan 40.
Gwamnati ta yi wannan karin ne bisa la’akari da karuwar al’umma, da rashin tsaro, da kuma sauran kalubale na sha’anin gudanar da mulkin masarautu a cewar kwamishinan.
Dangane da wannan kari, binciken wakilinmu ya nuna cewa, yanzu gwamnatin jihar za ta rika kashe Naira biliyan 3.1 a kan masarautun a duk shekara, a maimakon Naira biliyan 1.5 da ta saba yi a baya.