✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Game da kin biyan ’yan fensho na ‘New Nigerian’

Assalamu Alaikum. Edita ina so ka ba ni fili don na yi tsokaci a kan labarin da na karanta a Jaridar Daily Trust ta Turanci…

Assalamu Alaikum. Edita ina so ka ba ni fili don na yi tsokaci a kan labarin da na karanta a Jaridar Daily Trust ta Turanci a makon jiya, inda aka ruwaito wani Daraktan Kudi a ma’aikatar kudi ta tarayya ya danne hakkin ’yan fensho na kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke Kaduna. A labarin an nuna fiye da shekara daya kenan da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanya hannu a biya ma’aikatan Naira Biliyan 2 da miliyan 100 na wani bangare na hakkinsu, amma har yanzu abin ya ci tura. To abin tambaya a nan shi ne, anya Shugasban kasa Muhammadu Buhari ya san irin zagon kasar da ake masa na idan ya bayar da umarni a biya wasu hakkoki sai kuma wasu ko wani ya sanya kafa ya take? In ba haka ba ta ya ya za a ce shugaban kasa ya bayar da umarni sannan a samu wani mai mukamin Darakta wanda bai ma kai karfin Minista ba ya hana? Don haka ina kira ga masu fada a ji musamman a yankin Arewa da su sanya baki a wannan batu na ganin an biya ’yan fensho na kamfanin New Nigerian Newspapers da ke Kaduna hakkokinsu ba tare da bata lokaci ba. Da alama Buhari bai damu da irin zagon kasar da wasu ke yi masa da yankin Arewa ba. 

Nagode, sako daga Muhammad Sani Shokin, 08097015805.

A dawo mana da Nairar takarda

Assalam edita. Da fatan kana nan lafiya da ma’aikatanka. Allah Ya karo hazaka amin. Don Allah ina son ka mika mun kokena zuwa ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya dawo mana da Naira ta takarda, domin yin hakan zai kara farfado mana da tattalin arzikinmu. 

Daga Ibrahim Custom Sabon Gari, Zariya. 08035982540.

Game da ziyarar Buhari a Landan

 Assalamu Alaikum Editan Jaridar Aminiya. Muna yi wa shugaban kasarmu, Muhammadu Buhari fatar alheri a bisa ziyarar aiki da yake yi  a kasar Burtaniya, gabanin taron Common Wealth da za a yi a kasar a cikin wannan watan. Muna fata wannan zaiyara tasa ta zamo silar kulla kyakkyawan dangantaka mai karfi a tsakanin kasar ta Birtaniya da Najeriya ta fannoni da dama kamar su Diflomasiyya, kasuwanci da sauraran su. Duba da yadda Birtaniya ke laluben kasashen da za ta karfafa yin hulda da su a sakamakon shirin ficewar ta daga cikin kungiya Tarayyar Turai ta EU. Daga karshe, muna rokon Allah Ya kiyaye wannan tawaga ta shugaba Buhari a kasar London, Ya ba da sa’ar tafiya, sannan Ya kuma dawo mana da su gida lafiya. Amin Summa Amin. 

Daga Ado Salati Goma Ga Annabi Rijau da Shamsuddeen Abdullahi Makanike Rijau da Shehu Adamu Rijau, a Jihar Neja. 07085238454.

Matasa mu nisanci bangar siyasa

Assalamu Alaikum. Editan Jaridar Aminiya mai albarka dan Allah ka ba ni dama na yi kira ga ‘yan’uwana matasa maza da mata da lokaci ya fara tahowa na zaben 2019, da ya kamata mu kaucewa kabilanci da bangar siyasa, domin sune makamin da wadansu ‘yan siyasa suke amfani dasu wajen kaiwa ga nasara a zabe. ‘Yan uwa matasa idan muka duba menene ribarmu a tada rikici na kabilanci da bangar siyasa da muka yi muka taimakawa dan siyasa ya kai ga nasara a baya? Ya tuna da kai? Abin takaicin ma shi ne duk inda ka ji wata sa-in-sa to matasa ne sahun gaba, mu kashe junanmu, mu raunata junanmu, a turo jami’an tsaro su kama na kamawa su azabtar, wani sa’in ma su kashe na kashewa. Zaku ga cewa ba mu da wata riba sai dai da na sani, dan haka yan’uwana “kowa ya ki ji to fa ba ya ki gani ba”. 

Daga Aminu Adamu Malam Madori, Jihar Jigawa. 08182315298.

Takarar Lamido; Idan maye ya ci ya manta! 

Assalam edita. Ka ba ni dama domin na yi tsokaci dangane da neman takarar shugabancin kasa da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ke yi. Domin idan maye ya ci ya manta, to uwar diya ba za ta taba mancewa ba. Hakika mu ‘yan Jigawa muna yi wa kallon wannan takara tamkar abinda Hausawa ke cewa “Mai neman kahon kare ya wahala”. Domin mu ‘yan Jigawa shaidu ne, na yadda tsohon gwamnan  da ‘ya’yansa, suka mayar da dukiyar jihar tamkar wadda suka gada. Wadda har aka taba ambato shi yana cewa “Dukiyar Jigawa tamkar naman kifi ce, a raye halak, a mace halak”. Kuma wai irin wadannan mutanene wai yanzu suke neman takarar shugabancin kasa, to mu dai adduarmu Allah Ya tsari gatari da saran shuka. Kuma muna shaida wa mutane irinsu Sule Lamido da su sani cewa mu ‘yan Jigawa mun shirya tsaf wajen cigaba da wayar da kan al’ummar Najeriya dangane da illolin dake tattare da zabar mutane irinku wadda har yanzu ake tuhumarsu bisa amanar dukiyar alummarsu. Domin hakan tamkar tamkar mayar da hannun agogo baya ne, wajen kokarin da ake na magance matsalar cin hanci da rashawa da ta yi wa kasarmu katutu. 

Daga Isah Ramin Hudu Hadejia. 08060353382.

Kira ga Gwamnan Jigawa

Assalamu Alaikum zuwa ga gidan jaridar Aminiya Hausa, majiya mai tushe. A yau na shigo gidan ne domin na yi kira ga gwamnatinmu ta jahar Jigawa a bisa gyaran hanyar motarmu wacce ta tashi daga Sabuwar Gwaram ta wuce tsohuwar Gwaram ta hada da garin Darazo na Jahar Bauchi. Wallahi Mai Girma Gwamna wannan hanyar ta yi mummunar lalacewar da tafi gaban misaltawa, domin a sanadin lalacewar hanyar motar a yanzu haka wasu ‘yan kasuwar da suke fitowa daga jahohin Bauchi, Gombe, Adamawa da Taraba ta sa su dole canza hanya. Wanda hakan yake shafar kasuwancinmu. Dan haka muna sake tuni ga Gwamnanmu na Jahar Jigawa da ya yi wa Allah da Annabinsa ya waiwaice mu. Da fatan Allah Ya sa kiran zai je kunnuwan da suka dace. 

Sako daga Ashiru Usman Sabuwar Gwaram. 07030817573.

Kafa kwamitin binciken sojoji ya yi daidai 

Assalam edita. Ka ba ni dama in yi tsokaci game da Kwamitin da shugaban Hafsa sojoji kasa ya nada ya yi dai-dai a kan zargin da aki yi musu na nuna bambanci da nuna bangaranci na taimaka wa wasu ‘yan ta’adda domin kawar da wasu kabilu idan bincike ya nuna gaskiyan lamarin haka, ya ki, to a hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki, idan kuma ba haka ba, binciki ya nuna sharri ne ake musu . 

Daga Mustapha Saidu Mohammed Anka, [email protected], 08037558407

Buhari ya sauya zance!

Assalamu Alaikum. Fatan alheri a gare ku ma’aikatan Jaridar Aminiya mai farin jini. Don Allah Edita ka taimaka ka ba ni dama in yi waiwaye wanda Hausawa kan ce adon tafiya; A shekarar 2015 Shugaba Buhari ya ce shekara hudu kacal zai yi a kan mulki saboda yawan shekaru, sannan kuma zai bai wa sauran al’umma dama ta tsayawa takarar shugaban kasa! Amma sai ga shi kwatsam zance ya sauya, na bada sanarwar za ka sake tsayawa takara. Haba Baba Buhari, ga rashin aikin yi ga matasa ga talauci da ke damun al’umma, sannan matasa babu ilimi, ga kuma alfarma da ta baibaiye gwamnatoci. 

Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli Gidan Doki. 07068295953.

Godiya ga Buhari bisa amsa koken talakawa 

Salam. Don Allah Edita ka ba ni dama na mika sakon godiyata a madadin talakawa masu son ganin cigaban kasarsu ga shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari bisa yadda ya amince da kokenmu na ya kara tsayawa takara a karo na biyu. Tabbas mu talakawa mun ji dadi kuma mun amince idan ana mulki sau 10 to ya yi ta yi, domin mun gamsu yana kishinmu kuma yana son mu. Kawai yana gamuwa da tarnaki ne daga makiya cigaban kasa. Kuma insha Allah za mu zuba masa ruwan kuri’a fiye da wadda muka ba shi a 2019. 

Daga Shehu Mansur Sule Getso, Jihar Kano-07037079900.

Tambayoyi hudu ga Honarabul Garba Datti  

Assalam edita. Da fatan dukkanku kuna lafiya amin. Ina son ka ba ni dama in mika tambayoyi na hudu ga dan Majalisa mai wakiltar Mazabar Sabon Garin Zariya a Abuja wato, Garba Datti Babawo. Ko ka fara tunanin faduwa zabe? Ko ka san kujerar da kake kai ba ta gado ba ce? Ko kana ziyarar mazabarka? kudurori nawa ka gabatar don cigabanmu? 

Daga Lawal Muhammad, Tsohon Sakataren Taskfos NANTMP.

Hadin kan Arewa ne mafita

Salam Edita. Ina kira ga al’ummamu na yankin Arewa, musammam matasa, domin mu ne manyan gobe. Mu hada kai mu daina zagin junammu da cin zarafin shugabannimmu musamman a yanar gizo domin ba haka ‘yan Kudu su ke yi ba. Yanzu lokacin siyasa ne idan ba su yi mana abun kirki ba sai mu sauya su ta hanyar zabe cikin ruwan sanyi. 

Daga Uba Ahmed Balarabe KD.