Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG), ta bayyana alhininta bisa rasuwar mamallakin gidan Jaridar Leadership, Sam Nda Isaiah wanda ya rasu a ranar Juma’a yana da shekara 58.
CNG a wani sako da ta aike ta hannun kakakinta, Abdul-Azeez Suleiman ta ce hakika rasuwar Nda Isaiah, babbar rashi ne domin “sanannan masanin magunguna ne, marubuci, kuma kwararren dan siyasa”.
- ‘Yan bindiga sun sace tsohowa mai shekara 90 a Zamfara
- Hanyoyi 7 da za a bi domin magance sanko
- An gano likitan da yake zuba wa marasa lafiya maniyyinsa a mahaifa
Gamayyar ta kara da bayyana mamacin a matsayin dan kishin Arewa da yake fadi-tashi koyauahe a kan jama’ar yankin Arewacin Najeriya.
“Za a jima ba a cikin da aka samu da rasuwar babban jigo a wannan hadakar kungiyoyin ba tun lokacin da aka samar da it a.
“Mista Isaiah ya jima yana bayar da gudunmawar da goyon baya da karfafa gwiwa da bayar da shawara ga hadakar Kungiyoyin Arewacin Najeriya; hakika abun alfahari ne saboda shi ya daga darajar harkokin kungiyar,” kamar yadda aka bayyana.
Kungiyar ta yi wa ’yan uwa da abokanan arzi da makusanta da ma’aikatan dake karkashin marigayin fatan hakurin jure babban rashin managarcin abun koyi.