A ranar Asabar ta gabata 13 ga Afrilun nan ne Allah Ya yi wa Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi kuma Mai shari’a Mamman Nasir rasuwa bayan ya yi gajeruwar rashin lafiya. Marigayin wanda ya taba zama Shugaban Kotun Daukaka Kara ta Tarayya an yi jana’izarsa a wancan ranar a garin Malumfashi da misalin karfe 4:00 na yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Mai martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir na daga cikin dubabban Musulmin da suka halarci jana’izar marigayin.
Galadiman Katsina mai kimanin shekara 90 a duniya, ya rasu ya bar matan aure uku da ’ya’ya 13 da jikoki da dama. Kuma shi ne Ministan Shari’a na farko a tsohuwar Jihar Arewa lokacin mulkin su Firimiyan Arewa Sardaunan Sakkwato Alhaji Ahmadu Bello. A 1992 ne aka nada shi Galadiman Katsina na 10, bayan rasuwar dan uwansa Galadiman Katsina Alhaji Abdullahi Mahuta.
Wannan sarauta ta Galadima tana daga cikin manyan Hakiman Karaga a Masarautar Katsina domin yana daga cikin masu zaben sabon Sarki.
Marigayin kafin rasuwarsa, ya yi fice a fannoni da dama musamman a kan abubuwan da suka shafi fannin shari’a da harkokin kungiyoyin da ke kawo wa Arewa ci gaba. Kamar Kungiyar Kare Muradun Arewa wato ACF da sauransu.
Kamar yadda wata majiya ta bayyana, kafin rasuwarsa sai da wakilan kungiyar da yake yi wa jagoranci ta Gidauniyar Jihar Katsina suka kai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ziyara. Marigayin ya karbi shugabancin kungiyar ce daga hannun shi Shugaba Muhammadu Buhari.
A watannin baya masu garkuwa da mutane suka kai masa hari a hanyarsa ta dawowa gida daga Katsina, harin da ba su samu nasarar tafiya da shi ba sai suka tafi da Shamakinsa.
To ko me al’ummar Malumfashi za su rika tunawa game da marigayin har su rika yi masa addu’a?
Malam Shamsu Maishayi na daga cikin mutanen da suka ji wannan babban rashi na Galadima, ya ce “Gaskiya ba karamin rashi muka yi ba, domin Galadima garkuwa ne ga talakawan Malumfashi. Har abada ba za mu manta da wani abu da ya taba faruwa a tsakanin manoma da masu bayar da bashin noma ba inda a wancan shekara aka samu matsala a batun noma. Abin ya yi nisa har aka zo kama manoman da aka ba rancen kudin, amma marigayin ya yi ruwa-da-tsaki ya hana tafiya da kowa sai dai shi a tafi da shi.”
“Sannan na san kowace Juma’a yara na taruwa a kofar fadarsa ya fito yana ba su kudi, can gefe kuma ga layin dattawa su ma suna karba. Wani abin tunawa game da shi, shi ne a duk lokacin da kuka je gaishe shi, to sai an yi barkwanci an yi raha, a karshe kuma ya yi muku nasiha a kan ku tashi ku nemi na kanku kada ku dogara da wani. Wannan na daga cikin irin abubuwan da za mu ci gaba da tunawa da shi,” inji Shamsu Maishayi.
Kusan duk mutanen da aka tuntuba irin wadancan halayen suke tunawa da su game da rayuwar marigayi Galadiman Katsina wanda suka ce bai dauki duniya da zafi ba balle abin duniya ya dame shi.
Tuni Shugaban Kasa da gwamnoni da sarakuna da manyan ’yan siyasa da shugabannin jama’a suke ta aikewa da sakon ta’aziyya kan rasuwarsa.
Galadiman Katsina Mai shari’a Mamman Nasir babban bangon jingina ne da rasuwarsa ta zo bayan wasu makonni da rasuwar Dangaladiman Katsina Hakimin Kafur Alhaji Rabe Abdullahi wanda ya bar duniya yana da shekara 72. Shi ma ya rasu bayan ya yi fama da jinya. Dangaladiman Alhaji Rabe Abdullahi ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya da jikoki. Allah Ya jikansu da rahama, amin.