Wata sabuwar gada ta rushe kasa da mako guda da kammala aikin gina ta a Jihar Kogi.
Rushewar gadar a garin Ozuma, mahaifar Gwamna Yahaya Bello, ta jawo fargaba ga jama’ar Mazabar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Tarayya.
- Wasu ’yan Izala sun bijire wa Sarkin Musulmi, sun yi Idi ran Laraba
- Dalilin da Sheikh Dahiru Bauchi ya yi Idin Karamar Sallah
Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar PDP a Jihar Kogi, Dayo Onibiyo ya ya yi zargin an yi amfani da kaya marasa inganci a wajen gina Gadar Ozuma a yankin Okengwe, Karamar Hukumar Okene ta Jihar.
Ya yi zargin masu neman azurta kansu ta haramtacciyar hanya na neman jefa rayuwar matafiya cikin hadari ta hanyar gina gadar wadda ya kamata ta saukaka musu zirga-zirga.
Ya kuma yi zargin cewa a shekara biyar na Gwamnatin Yahaya Bello, har yanzu ta kasa kammala aiki guda daya.
“Muna shawartar Yahaya Bello ya yi koyi da PDP da yadda ta kammala aikin gadar Meme mai kaurin suna da sauran ayyukan da rashinsu ke jefa rayuwar mutane cikin hadari,” inji shi.
Jami’in na PDP ya bukaci Hukumar Kula da Ingancin Kaya da Kungiyar Injiyoyi ta Najeriya da su yi binciki rushewar gadar da Gwamnan ya yi da kuma tabbatar da cewa duk muhimman ayyuka da ake yi a jihar sun cika ka’idojin da suka dace.
“Muna kuma tsoro kar irin haka ya faru da aikin gadar sama ta Gajana a Lokoja, saboda gadar da ba ta kai ta ba ma ta karye kafin sati daya kammala aikin.” inji sanarwar da ya fitar.