✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaba da gabanta

Wani muhimmin abin da ake ta fadi game das hi a fagen siyasar kasar nan shi ne batun yin amfani da sojoji don gudanar da…

Wani muhimmin abin da ake ta fadi game das hi a fagen siyasar kasar nan shi ne batun yin amfani da sojoji don gudanar da zabubbuka masu zuwa. An fara wanan maganar ce da kuma nuna damuwa game da ita tun bayan kammala zaben gwamnan Jihar Ekiti a shekarar da ta gabata yayin da aka jajibo sojoji aka jefa su cikin badakalar zaben gwannan jihar. Jama’a da yawa sun nuna rashin amincewarsu da haka, don rashin dacewarsa, domin zargin da aka yi na cewa sojojin sun taimaka wajen samun nasarar dan takarar jam’iyyar PDP sa’ilin da suka mamaye jihar don yi wa mutane barazana da kuma tsorata su, har suka kaurace wa tashoshin jefa kuri’a, abin da ya bayar da damar taimaka wa jam’iyyar PDP ta tafka magudin da ya kai dan takararta ga samun nasara.

A bisa gaskiya shigar da sojoji a harkokin zaben Jihar Ekiti ya tayar da kura ainun, kuma har gobe jama’a ba za su taba mancewa da mummunar abin da ya faru dangane da haka ba, domin kuwa wasu askarawan da suka lullube kawunansu da kokuwa sun aikata ta’asa son rai, sun kuma tsoma bakunansu cikin harkokin zabe ba tare da la’akari da abin da zai je, da wanda zai komo ba. Asirin haka ya tonu sa’ilin da aka fitar da wani faifan labarai dauke da muryoyin manya-manyan hafsoshin soji da hamshakan siyasa suna kulle-kullen dabaraun murde wa zaben Jihar Ekiti, kuma daga bisani dukkansu sun amince cewa muryoyinsu ne aka nada, kuma suka amince da dukkan abubuwan da aka ji suna furtawa. Amma abin takaici game da haka shi ne gwamnati ko kuma wata hukumar da ke karkashinta ba su nuna sha’awarsu na binciken wannan zargi ba da niyyar hukunta wadanda suka aikata ta’asar da ake zargi.
Wannan ya tabbatar da dalilan da suka sa yawancin ‘yan Najeriya ba su kaunar yin amfani da sojoji yayin zabe tun da sun rigaya sun fahimci irin rawar da aka ce sun taka wajen kai wa ga biyan bukatar jam’iyyar da ke da gwamnatin tarayya, ta hanyar daure gindi don aikata manyan laifuffukan da suka shafi magudin zabe. A ko ina a duniya jama’a sun yi amanna cewa babu ruwan sojoji da al’amuran da suka jibanci gudanar da zabe domin kuwa akwai ‘yan sanda wadanda aka dora musu hakkin tabbatar da tsaro da kuma kare dukkan masu jefa kuri’a da kawo zauna lafiya.
Dangane da haka ne ma Kotun daukaka kara ta yanke wani hukunci a ranar 16 ga watan jiya a wata kara game da zaben Mr Ayodele Fayose a matsayin Gwamnan Jihar Ekiti, inda ta fayyace cewa shigar da sojoji cikin harkokin zabe ba shi bisa ka’ida domin kuwa hakan ya saba ka’idojin kundin tsarin mulkin kasar nan. Sakamakon wannan hukuncin ne kuma jam’iyyar adawa ta APC ta fadakar da Shugaba Goodluck Jonathan da kuma Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega game da hukuncin, ta kuma ce wajibi ne su amince da ita. Haka nan kuma jam’iyyar ta kara janyo hankalin gwamnatin tarayya game da wani hukuncin da Mai Shari’a R.M. Aikawa ya yanke a Babbar Kotun Tarayya ta Sakkwato a ranar 29 ga watan shekaran jiya, wacce a ciki ya haramta yin amfani da sojoji a lokutan da ake gudanar da zabe.
Amma baicin haka nan sai ga jam’iyyar PDP ta fandare, ta ce ita ba abin da zai sa ta canja ra’ayinta game da amfani da sojoji a zabubbuka masu zuwa. Ministan Al’amuran ‘Yan sanda, Alhaji Jelili Adesanya ya fayyace wa manema labarai a Jihar Osun cewa, gwamnatin tarayya za ta yi amfani da sojoji a zabubbukan watan nan da kuma na Afrilu, domin kuwa ba za ta bari makiya zaman lafiya su dagula al’amura ba. Ya ce yawan ‘yan sandan da ake da shi bai isa ba su yi wannan aikin, kuma sai byan zabe ne za a kara daukar wasu guda dubu 25.
Talakwan Najeriya dai sun dage wajen tabbatar da cewa nacewar da gwamnatin tarayya ta yi don amfani da sojoji a lokutan zabe ya nuna yadda jam’iyyar PDP ta kidime, ta kuma dukufa wajen yin amfani da sojoji don tafka magudin zabe ko ta halin kaka. Abin da Minista Jelili Adesanya ke cewa shi ne gwamnatin tarayya da jam’iyyarta ba su da niyyar aiki da hukunce-hukuncen kotuna dangane da amfani da sojoji a ranar zabe. Baicin zargin da aka yi wa sojoji na tafka magudi a badakalar da aka yi a Jihar Ekiti a bara, wanda wani Kyaftin na soja ya yi tonon silili akai, kotunan kasar nan sun haramta yin amfani da sojoji a lokutan zabe.
Tilas ne fa gwamnatin tarayya ta amince da wadancan hukunce-hukuncen, ta kuma guji fitar da sojoji a ranakun zabe, ta bar su can a barikokinsu don ayyukan tsaron kasa. Muddin dai ba gwamnatin tarayya na son ta ci gaba da mike kafa ne ba bisa karagar mulki ko ta halin kaka, to ya wajaba a gare ta ta bi umurnin kotuna idan dai ba tana so ta jefa kasar cikin wani bala’i ne ba. A takaice dai ana iya cewa abin da Minista Jelili ke cewa shi ne Gwamnatin Jonathan ba za ta bi wancan umurnin ba. To idan har gwamnatin tarayya ba za ta yi aikin da hukuncin kotuna ba, ina amfaninsu ke nan; kuma ba sauran wanda zai sake bin doka da oda a kasar nan, sai dai kawai ya aikata son zuciyarsa? Jam’iyyar PDP na tinkaho cewa ita ce giwar siyasar nahiyar Afirka, kuma babu wanda ya isa ya ja da ita a nan cikin gida, to kamata ya yi ta san cewa gaba da gabanta, kuma komai karfinta ba ta kai na shari’a ba.