Fitaccen jarumin fina-finan Hausa da na Kudancin Najeriya, Nuraddeen Muhammed Usman, wanda aka fi sani da Nura MC Khan ya ce matsalar fyade annoba ce, wadda a cewarsa ta fi annobar coronavirus.
A zantawarsa da Aminiya, jarumin, wanda kuma shi ne shugaban masana’antar shirya fina-finai ta Kaduna (Kadawood), ya ce ya kamata a rika dandake masu yi wa kananan yara fyade.
- ‘An kama fasto ya yi wa ‘yar shekara 12 fyade’
- Fyade: Kotu ta tsare Mai Siket a gidan yari
- An tsinci gawar ‘yar shekara shida an yi mata fyade a masallaci
“Mu a masana’antar Kadawood, mun fito ne domin mu yi Allah wadai da wannan mummunar annoba da bala’i da ta
addabi alumma. Hakikanin gaskiya, gaskiya fyade babbar annoba ce da ta fi coronavirus.
Kananan yara sun fi shiga hadari
“Fyaden da ake yi yanzu ya sha bamban da irin wanda ake yi wa manyan mata a da. Yanzu kananan yara ne daga wadanda aka haifa, zuwa wandan suka fara tasawa ake yi wa.
“Wannan babban bala’i ne, kuma ba ma jin dadi, kuma duniya baki daya ta yi tir da wannan abu…Fyade bala’i, annoba ce, masifa ce, kuma kowane mutum mai hankali ba zai so shi ba tun daga kan iyaye har zuwa yara”, inji shi.
Sakacin wane ne?
Da aka tambaye shi ko akwai laifin iyaye, sai ya ce, “Na farko ina kira ga iyaye mata da maza da mu sa ido kan yaranmu, musamman kananan yara.
Ya kamata iyaye su san abokan yaransu, kuma su san ina suke zuwa, kuma su san wane ne za su bari da yaran. Kuma su rika sanin irin tarbiyar wadanda za su bari da yara.
An samu inda dan uwa ya yi ’yar uwarsa fyade yanzu. Yanzu babu amana, don haka dole a sa ido sosai.
Me ya kamata a yi wa masu fyade?
A game da hukuncin da ya kamata a rika dauka kan masu fyade, jarumi Nura MC cewa ya yi, “Gwamnati na iyakan kokarinta wajen daukar kwawaran matakai, amma abin da nake ganin ya fi kamata, wanda kuma mutane suka fi karkata shi ne ko mutum babba ne ko karami, idan aka kama shi yana yi wa karamar yarinya fyade, to a dandake shi kawai. Idan aka wa kamar mutum 10 haka, to kowa zai shiga taitayinsa.”
Nuna tsiraici na taimakawa
Da ya juya kan mata, musamman manya, ya ce irin shigar da suke yi na tsiraici da sanya hotuna masu nuna tsiraici da wasu ke yi a kafafen sadarwa na zamani yana taimaka wajen sanya mutane sha’awarsu, wanda idan mutum ya nemi hadin kansu bai samu ba, sai ya nemi mata fyade.
Daga karshe sai ya ce, “mu a masana’antar Kadawood, muna tir da wannan hali da wasu ke yi, kuma fata za a rika yanke hukunci a kan wadanda aka kama.”