✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fyade: Kotu ta daure mutumin da ya yi luwadi da ’yar cikinsa

Ya yi wa ’yar cikinsa fyade sau biyar, tare da yin luwadi da ita

Kotu ta yanke wa wani magidanci da ya yi wa ’yar cikinsa mai shekara 14 fyade ta hanyar luwadi hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari.

A ranar Alhamis kotun da ke zamanta a Jihar Akwa Ibom ta yanke hukuncin bayan samun sa da laifin azabtarwa da kuma yi wa ’yar cikinsa fyade sau biyar a lokuta daban-daban cikin shekara daya.

Yarinyar ta shaida wa babbar kotun jihar cewa mahaifin nata mai suna Uduak Abasi Oku Edet, ya taba yin luwadi da yarinyar ta karfin tsiya, lamarin da ya sa ta kasa yin bayan gida.

Ya kuma sha zane ta da bulala, sannan ya taba daba mata wuka a kai, saboda ta dauki abinci ba tare da izinin matarsa ba.

Yarinyar ta shaida wa kotun cewa fyaden da mahaifin nata ya yi mata ya sa ta rika jin radadi da wasu sauye-sauye a jikinta.

Bayan sauraron shaidun masu gabatar da kara, Kungiyar Lauyoyi Mata ta Duniya (FIDA), wadda ta kai wa ’yan sanda rahoto kafin gurfanar da Uduak Abasi Oku Ede, alkalin kotun, Bassey Nkanang ya yanke wa mutumin hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari.

%d bloggers like this: