✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fusatattun mutane sun hallaka mutumin da ake zargi da kona Alkur’ani a Pakistan

Tuni dai aka kama mutane da dama da ake zargi da hannu a kisan.

Wasu fusatattun mutane sun hallaka wani mutum da ake zargi da kona Alkur’ani ta hanyar lakada masa dukan tsiya a garin Khanewal da ke lardin Punjab na kasar Pakistan.

Mutane da dama ne ya zuwa yanzu aka tabbatar da kama su kan kisan mutumin, wanda ya faru ranar Asabar a garin, kamar yadda wakilin Fira-Ministan kasar kan Harkokin Addini, Tahir Ashrafi, ya tabbatar.

Kazalika, jami’an tsaro na can suna ci gaba da farautar sauran masu hannu a kisan mutumin.

’Yan sanda dai a lardin na Punjab sun ce akalla mutum 15 ne suka shiga hannu, yayin da ake ci gaba da farautar kusan mu 85.

Fira-Ministan kasar, Imran Khan dai ya ba da umarnin daukar mataki a kan dukkan masu hannu a cikin ta’asar, ciki kuwa har da ’yan sandan da lamarin ya faru a kan idanunsu, amma suka ki yin katabus.

“Za mu dauki tattsauran mataki a kan lamarin tare da tabbatar da cewa doka ta yi halinta. Ba za mu kyale mutane su rika daukar doka a hannunsu ba,” inji Fira-Ministan a cikin wata sanarwa.

Kisan na zuwa ne kusan wata biyu bayan an lakada wa wani manajan masana’anta dan asalin kasar Sri Lanka dukan tsiya har sai da ya mutu, shi ma saboda aikata batanci.

Mutanen dai sun hadu a wani masallaci ne ranar Asabar da daddare bayan dan wani limami ya ce ya ga wanda ake zargin yana kona wasu shafuka na Alkur’anin, kamar yadda wani jami’in dan sanda, Munawar Hussain ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ya ce lokacin da ’yan sanda suka isa wajen, sun iske mutumin daure a jikin bishiya ba ya iya ko motsi, inda ya ce su kansu ’yan sandan sai da mutanen suka kai musu hari.