Kungiyar kwallon kafar Fulham ta kammala daukar dan kwallon Brazil, Andreas Pereira daga Manchester United.
Kungiyar da ke birnin Landan ba ta fayyace kan nawa ta dauki dan kwallon ba, amma an fahimci cewar cinikin ya kai fam miliyan 10 har da karin tsarabe-tsarabe.
Sai dai Fabrizio Romano, fitaccen dan jarida wanda kuma ya shahara a kan fashin baki da tattara bayanan lamurran da suka shafi sauyin shekar ‘yan wasa, ya ce United ta cefanar da Pereira a kan fam miliyan 10 (£10m) da karin tsarabe-tsarabe kimanin fam miliyan uku.
Pereira mai shekara 26 ya saka hannu kan kwantiragin kaka hudu tare da kungiyar da Marco Silva ke jan ragama, wadda za ta buga Firimiyar Ingila a kakar nan, bayan da ta lashe Championship a kakar da ta wuce.
Andreas Pereira shi ne na biyu da Fulham ta saya a bana, bayan Joao Palhinha daga Sporting kan fam miliyan 17.