✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fulani sun fi kowa shan wahalar masu garkuwa da mutane – Bagudu

Bagudu ya ce babu wanda yake jin ko labarin nasu bangaren.

Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya ce al’ummar Fulani sun fi kowa shan wahalar ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da masu satar shanu a Najeriya.

A yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, Gwamna Bagudu ya ce babu wanda yake jin irin halin da Fulanin da aka sace su ko aka dauke musu dabbobi suke ciki.

A lokuta da dama dai an sha zargin Fulanin da cewa suna da hannu dumu-dumu a a satar mutane da sauran ayyukan ta’addanci, ko da dai sun sha musanta hakan.

A cewar Gwamnan, akwai Fulani da dama da suke son zama da sauran jama’a amma mutane da dama ba sa son jin nasu bangaren labarin.

“Na gana da yankunan Fulani da dama a Jihata kuma sun min bayanin cewa suma lamarin na shafarsu. Su aka fara sacewa ana kwashe wa dabbobi.

“Duk wanda ke ta’ammali da miyagun kwayoyi, zai fi masa sauki ya shiga yankin da babu hanya mai kyau, babun ’yan sanda babu sauran kayan more rayuwa ya sace dan uwansa ko ’yar uwarsa ya bukaci a sayar da saniya a bashi kudin fansa.

“Su suka fi shan wahalar ayyukan ’yan bindiga, yayin da sauran ayyukan garkuwa da mutane Fulani da wadanda ba Fulani ba suka hada gungu domin aiwatar da muguwar sana’ar tasu.

“Kazalika, in ka dubi satar shanu da ake wa makiyaya, za ka ga kusan dukkan wadanda abin ya shafa Fulani ne.

“Babu ma wanda yake jin ko labarinsu. Ba ma jin nasu bangaren. Kawai kudin goro muke musu. Yawancinsu mutanen kirki ne masu son zaman lafiya,” inji Gwamna Bagudu.