Kungiyar Everton ta bai wa tsohon dan kwallon tawagar Ingila kuma tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea, Frank Lampard aikin horar da ita.
Lampard, mai shekara 43, bai da aiki shekara daya kenan, tun bayan da Chelsea ta sallameshi a Janairun bara, bayan wata 18 da ya horar a Stamford Bridge.
Everton ta sake ganawa da Vitor Pereira da kuma mai aikin rikon kwarya, Duncan Ferguson a karo biyu don zabar daya daga ciki, amma kungiyar ta sanar da nada Lampard.
An kori Rafael Benitez daga jan ragamar kungiyar, bayan da ya ci wasa daya daga 13 da ya fafata a bayannan.
Tsohon kocin Liverpool ya yi aikin kasa da wata bakwai, inda Everton ke mataki na 16 a kasan teburi da tazarar maki shida tsakaninta da ’yan ukun karshe.
Tun farko Everton ta yi niyyar bai wa Vitor Pereira Pereira aikin kocin, daga baya magoya baya da yawa suka taru a Goodison Park, wadanda suka ce ba sa bukatar Pereira a dauki Lampard.
Haka kuma ranar Laraba wasu magoya baya kimanin 100 sun gudanar da zanga-zanga a Goodison kan yadda ake gudanar da Everton.
Tsohon dan wasan Everton, Wayne Rooney ya samu damar zama kociyan kungiyar, amma bai je tattaunawa da mahukuntan ba, bayan da ya zabi ci gaba da aiki da Derby mai buga Championship, wadda ba ta yin kokari a kakar nan.