A farkon wannan mako ne sama da mutum dubu 100 suka canja sheka daga jam’iyyun APC da PDP zuwa Jam’iyyar SDP a Jihar Adamawa.
Shugaban Jam’iyyar SDP ta kasa, Cif Olu Falae ne ya bayyana haka a lokacin da suka je taron karbar Cif Emmanuel Bello zuwa Jam’iyyar SDP wanda aka yi a gidan silima na Lamido Cinema da ke Yola.
“Na halarci wannan taron ne domin karbar Cif Emmanuel Bello da mutum sama da dubu 10 wadanda suka gaji da zalunci da wulakanci suka canja sheka daga jam’iyyun PDP da APC zuwa inda za a yi musu adalci a wannan jam’iyyar tamu ta SDP,” in ji shi.
“A yau na shaida cewa sun zama mambobinmu a Jam’iyyar SDP,” inji shi. Ya ce Jam’iyyar SDP ta samo asali ne tun lokacin marigayi MKO Abiola da Babagana Kingibe a 1993. Cif Falae ya kara da cewa Bello mutum ne wadda ya yi imanin zai iya canja canjin sauran jam’iyyun.
Haka tsohon Minista, Jerry Gana wanda ya kasance daya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar ta SDP ya ce, wannan shi ne fitarsu ta farko a bana, inda ya kara da cewa jirgin SDP ya zo ne domin sada Najeriya da ci gaba a harkoki daban-daban.