✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu za ta rataye matashi kan kisan karuwa

Kotu ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 26 hukuncin ratayewa kan laifin kashe wata karuwa bayan ya yi lalata da ita

Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kan laifin kashe wata karuwa bayan ya yi lalata da ita.

Babban Kotun Jihar Ekiti ce ta yanke masa hukuncin bayan an gurfanar da shi kan zargin haɗa baki da kuma garkuwa da matar da kuma amfani da maganin kashe ciyawa wajen halaka ta a ranar 18 ga Afrilun 2024.

Tun da farko mai gabatar da ƙara, Ibironke Odetola, ya bayyana wa kotun a ranar 6 ga watan Fabrairu, cewa wanda ake zargin ya haɗa baki d da wani abokinsa wajen sace matar da ke sana’ar kasuwanci.

Wanda ake zargin, David Isaiah, mai shekara 26, ya shaida wa kotun cewa bayan ya yi lalata da matar ne ya yi amfani da wayarta ya kira abokan sana’arta da cewa an yi garkuwa da ita, sai an kawo kuɗin fansa Naira 100,000.

A yayin da yake karanta hukuncin, Mai Shari’a Lekan Olatawura, ya yanke wa wanda aka gurfanar da laifin garkuwa da mamaciyar.

“Don haka an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 21 kan laifin haɗin baki kan laifin garkuwa da mutane. Game da laifin kisa kuma kotu ta yanke mas a hukuncin ratayewa har sai ya mutu,” in ji alƙalin.