Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce zuwa yanzu fiye da mutum 4,000 ne suka yi rajista don neman shiga shirin auren zawarawa na jihar wanda za ta yi nan da mako biyu.
Hukumar ta ce ta tace mutum 1,800 wadanda kuma aka shirya tantance lafiyarsu a mako mai zuwa.
- Babu abin da Ganduje zai tsinana wa Tinubu a 2027 — Kwankwaso
- Ukraine ta roki UEFA kar ta dawo da Rasha cikin wasannin Turai
Da yake jawabi ga Aminiya, Mataimakin Kwamanda Janar na Bangaren Ayyuka, Dokta Mujahid Aminuddedn ya ce dole ma’auratan su zama ba su dauke da cuta mai karya garkuwar jiki, sannan dole a san nau’in jininsu da kuma yi musu gwajin kwayoyi halitta.
Dokta Mujahid ya kara da cewa, “Gwamnati ta shirya aurar da mutum 1,800, amma sai ga shi an samu fiye da mutum 4,000, don haka muka sanar da Gwamna halin da ake ciki, inda ya amince a shigar da su a karo na biyu na auren.”
A jawabin Mataimakiyar Kwamanda Janar, Bangaren Mata Dokta Khadija Sagir Sulaiman ta yi karin haske game da Naira miliyan 22 da hukumar ta ware don yin shagalin bikin auren kamar yadda Babban Kwamandan Hukumar Malam Ibrahim Daurawa ya bayyana a kwanakin baya.
Ta bayyana cewa, ‘‘Ba wai an ware wannan kudi don yin walima kadai ba ne, za a hada da ayyukan bita da kuma koyar da sana’o’i ga ma’auratan.
Ta ce, “Mutane na ta surutu cewa an ce za a rakashe a wajen bikin, ai ana nufin za a yi walima wanda kuma kowa ya san muhimmancin walimar aure a addinin Musulunci.
“Kuma matan nan a junansu za su yi kidan kwarya su cashe da junasu ba tare da maza sun shiga wurin ba.
“Don haka wadannan kudi za a kashe su a wajen shirya wa ma’auratan bita ta tsawon kwana uku.
“Haka kuma za a koyar da matan sana’o’in hannu irin su hada man shafawa da sabulu da sauransu.
“Idan an duba dukkan wadannan abubuwa ne da suke bukatar kudi.”
Mafi yawan wadanda za a daura wa auren da Aminiya ta zanta da su, sun nuna farin cikinsu ga wannan shiri na auren zawarawa, inda suka gode wa Gwamann Kano saboda damar da ya ba su wajen yin aure a rayuwarsu.
Wani da ke sana’ar Keke NAPEP, mai suna Auwalu Ibrahim Sharada da Saliha Magaji sun ce, sun dade suna soyayya da juna, amma abin ya gagara duba da halin talauci da ya dabaibaye su.
Su ma Sabi’u Rabi’u da Hannatu Abba sun yi alkawarin zama lafiya da juna idan suka yi auren.