Daga Hudubar Sheikh Khalid bin Ali Al-Ghamidi
Masallacin Harami na Ka’aba da ke Makka
Bayan hamdala da taslimi:
1) Limamin ya fara da karanta “Al-khudbatul Hajah” wacce Manzon Allah (SAW) yake fara Huduba da ita a kowane lokaci.
2) Limamin ya tunatar a kan muhimmancin takawa da fadin cewa: Lallai bayin Allah masu takawa su ne mafi darajar bayi a wurin Allah. Kuma Allah Ya yi alkawarin taimakon bayinSa masu takawa kuma Zai ba su mafita. Allah (Subhanahu Wata’ala) yana cewa: “Duk wanda ya yi takawa, Allah Zai sanya masa mafita, kuma Zai azurta shi ta inda ba ya zato.”
3) Lallai Musulmi, wato al’ummar Manzon Allah (SAW) suna cikin fitintinu da kalubale masu yawa. Har rauni ya fara shiga zukatan wadansu suna cire tsammnin nasara ko gyaruwar al’amura, ganin lallai ana ta kashe Musulmi da yawa a sassan duniya.
4) Babu kokwanto Musulmi suna cikin kunci na yawan kashe-kashe ana ta korarsu daga gidajensu cikin cin mutunci da wulakantarwa.
5) Ya ’yan uwa Musulmi! Lallai Allah Ya hana masu imani su rika jin rauni a zukatansu a duk lokacin da wata jarrabawa ta same su. Allah Yana cewa: “Kada ku yi rauni, kada ku yi bakin ciki, ku ne madaukaka idan kun kasance masu imani.”
6) Musulmi mu tuna, ina makiya na farko? Ina Fir’auna? Ina Adawa? Ina sauran makiya? Shin sunanan ko kuma sun shude?
7) Lallai muna da daraja mai girma tunda mu al’ummar Manzon Allah (SAW) ne.
8) Lallai ba ya halatta mu rika jin rauni, tare da cire tsammanin gyaruwar al’amura, saboda kisa da korarmu da ake yi daga gidaje da kasashenmu.
9) Allah Ya yi mana alkawarin za mu yi nasara, kuma za mu samu rinjaye, sannan kuma za mu samu daukaka a duniya idan har mun yi imani da Shi (imani na hakika).
10) Mu rika tuna cewa wannan al’umma lallai Allah Zai taimake ta.
11) Fitintinun da muke ciki, Allah Yana sanya mu a cikinsu ne don Ya taimake mu.
12) Mu tuna cewa babbar darajar da Allah Ya yi mana kan al’umomin da suka rigaye mu ita ce, Allah Ya ba mu Annabi Muhammad (SAW) a matsayin Manzonmu.
13) Allah Ya yi wa wannan al’umma ta Manzon Allah (SAWA) karamomi da yawa a rayuwa.
14) Annabi (SAW) yana cewa: “Za ku cika al’ummomi guda saba’in” (dabaraniy ya ruwaito shi).
15) Allah Ya yi mana Karama da zama “Ummatun Wasadan” wato al’umma zababbiya kuma wadda take tsaka-tsakiya a cikin al’amura da ibada.
16) Allah Ya yi mana Karama da dauke mana abubuwa da yawa da suka shafi al’ummomin da suka rigaye mu.
17) Yana daga cikin karamomin da Allah Ya yi mana cewa, al’ummar nan ba za ta taba tabbata a kan bata ba har abada.
18) Allah Ya yi mana Karama da kare mana Alkur’ani daga lalacewa da tauyewa da gurbacewa. Duk wanda ya yi kokarin jirkita Alkur’ani, Allah Zai wulakantar da shi.
19) Allah Ya yi mana Karama da cewa duk bayan shekara dari, Zai tayar da wani muhimmin mutum da zai jaddada addinin Musulunci a bayan kasa.
20) Allah Ya yi mana Karama da cewa muna da karancin shekaru a bayan kasa idan an kwatanta da wadanda suka gabace mu, amma kuma albarkar rayuwar da Allah Ya ba mu ta fi tasu.
21) Allah Ya yi mana Karama da cewa mafiya yawan tsawon kwanakin da yake ba mu shi ne shekara 60 zuwa 70, sai kadan ne suke ketare haka. Amma kuma Ya cika su da ibadu da za mu yi mu samu lada mai yawa (kamar falalar Daren Lailatul kadar).
22) Allah Ya yi mana Karama da ninka mana lada a sallolin da muke yi a Masallaci Mai alfarma na Makkah da Masallacin Annabi (SAW) da ke Madinah da Masallacin Aksa da ke kudus.
23) Allah Ya yi mana Karama da cewa wannan al’umma, al’umma ce da za a yi mata rahama a Lahira, kuma ba ta da azaba a duniya (kamar yadda aka yi wa al’ummomin da suka gabata ta hanyar hallaka su da kifewa ko tsawa da sauransu) sai dai za ta hadu kashe-kashe da fitintinu kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya fada.
24) Allah Ya yi mana Karama da albarkatun kasa (kamar man fetur da zinari da azurfa da sauran abubuwa wadanda ba duk al’ummomi ba ne su ka same su.
25) Allah Ya yi mana Karama da sauki a cikin addini. Allah Yana cewa: “Allah Yana nufin sauki a gare ku, kuma ba Ya nufinku da tsanani…” Haka Annabi (SAW) yana cewa: “Ina nufin sauki ne gare ku, kuma ba na nufin tsanani. (Ahmad ya ruwaito).
26) Allah Ya yi mana Karama ta yafe mana duk aikin da muka yi bisa kuskure ko aka tilasta mu a kan aikatawa ko muka yi bisa mantuwa.
27) Allah Ya yi mana Karama da Sallar kasru. Wato Azahar raka’a biyu, La’asar raka’a biyu da Isha raka’a biyu, (yayin da muke cikin halin tafiya da ta kai wani munzali).
28) Allah Ya yi mana Karama da Sahur lokacin Azumi, kuma ya zama abinci mai albarka wanda Ahlul Kitabi ba su samu ba.
29) Allah Ya yi mana Karama da halattar mana ganima daga dukiyoyin abonkanen gaba da addininmu ba daya ba.
30) Allah Ya yi mana Karama da duk wanda ya rasu ranar Jumu’a ba za a yi masa azaba ba a kabari, sannan babu tambayar kabari a kansa.
31) Allah Ya yi mana Karama da cewa “Ribadi” wato gadin Musulmi da dukiyoyinsu, ya fi duniya da abin da ke cikinta.
32) Allah Ya yi mana Karama da cewa cutar annoba rahama ce gare mu.
33) Allah Ya yi mana Karama da cewa matar da ta rasu a lokacin haihuwa ta yi Shahada.
34) Allah Ya yi mana Karama da cewa duk wanda ya rasu yana kare iyalansa ko dukiyarsa ko addininsa ya yi Shahada.
35) Allah Ya yi mana Karama cewa rasuwa a sanadin cutar Tarin Fuka (Tuberclosis) Shahada ce.
36) Allah Ya yi mana Karama da cewa rasuwa a cikin ruwa Shahada ce.
37) Allah Ya yi mana Karama da cewa a cikin wannan al’umma mutum dubu saba’in ne za su shiga Aljanna babu hisabi babu azaba.
38) Allah Ya yi mana Karama, cewa an ‘kara mana daga mutum dubu 70 zuwa biliyan 4 da miliyan 900. Wato kowane mutum daya ya koma mutum dubu 70.
39) Allah Ya yi mana Karama da kasancewar Shugaban Dattawan Aljanna yana cikinmu. Wato Sayyidina Abubakar Siddik (Allah Ya kara masa yarda).
40) Allah Ya yi mana Karama da cewa Shugabannin Matasan Aljanna, Sayyidina Hassan da Sayyidina Hussain suna cikinmu.
41) Allah Ya yi mana Karama da cewa Shugabar Matan Ajanna wato Nana Fatima tana cikinmu.
42) Allah Ya yi mana Karama da cewa Shugaban Shahidai, wato Sayyidina Hamza yana cikinmu. (Allah Ya kara musu yarda dukkansu).
43) Wajibi ne mu yi kokari yin aiki mu tabbatar da cewa kada wadannan karamomi su zama dalilan rauni gare mu, sai dai su zama dalilan kara yin kokari da juriya wajen yin biyayya ga Allah.
44) Komai yana da sababi, don haka mu dage da bautar Allah sosai.
45) Duk wanda ya yi wa Annabi Muhammad (SAW) salati daya, tabbas Allah Zai yi masa guda goma.
46) Ya Allah Ka kara yadda da Sahabbai dukkansu. Ya Allah Ka kara yadda da Abubakar da Umar da Usman da Aliyyu (Allah Ya yarda da su dukka).
47) Ya Allah Ka taimaki Musulunci da Musulmi.
48) Ya Allah Ka kare garuruwanmu masu alfarma daga dukkan sharri.
49) Ya Allah Ka dawo da aminci a Syria da Palasdinu da Yemen da sauran kasashe da garuruwan Musulmi.
50) Ya Allah Ka taimaki “Waliyyu Amrina” wato Khadimul Haramain da mataimakansa guda biyu zuwa ga aikata abin da da Kake so, kuma Ka yarda da shi. Ka taimake su a kan aikin nagarta da takawa.
51) Ya Allah Ka taimaki sojojinmu da suke kan iyaka da sojojin Musulmi a ko’ina suke.
52) Ya Allah muna rokonKa don sonKa, da son duk abin da Kake so.
53) Lallai Allah Yana umurni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta hakkinsa, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki. Yana yi muku wa’azi tsammaninku kuna tunawa.
Ya Allah Ka ba mu ikon aiki da wannan nasiha, kuma Ka amsa mana addu’o’inmu.
Sheikh Khalid bin Ali Al-Ghamidi, ya gabatar da wannan Huduba ce a ranar Juma’ar da ta gabata, 3 ga Jimada Ula, shekarar 1437 Bayan Hijira daidai da 12 ga Fabrairu, shekarar 2016, Miladiyya