✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fitattun mutane 9 da suka taba rasa ‘ya’yansu

Davido ne na baya-bayan nan da ya rasa dansa mai shekara uku kacal a duniya.

Mutuwa dai na kan kowane mai rai, wato ko ba dade ko ba jima dole ne dukkan wani mai rai sai ya dandani mutuwa.

Bayan rasuwar da ga fitaccen mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, hakan ta sa Aminiya ta yi waiwaye tare da duba wasu mashahuran mutane musamman a fagen nishadi da suka taba rasa ‘ya’yansu.

1. Olu Jacobs da Joke Silva

A wata hira da ta taba yi a 2018, fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayo Joke Silva, matar Olu Jacobs, ta ce ta rasa ‘yarta ta fari, Dayo Jacobs, mai shekara 10 a duniya.

Joke Silva ta bayyana cewa ’yarta ta shafe watanni da dama a sume saboda rashin lafiya da ta sha fama da ita.

2. Remilekun Oshodi

Jarumar Nollywood, Remilekun Oshodi, wacce aka fi sani da Remi Surutu, ta rasa diyarta ta fari, Ayo Oshodi, a ranar 2 ga watan Yuli, 2017.

An rawaito Ayo mai shekara 16 ta sha fama da ciwon amosanin jini, wanda hakan ya zama ajalinta.

3. Mista Ibu

Fitaccen jarumin fina-finan barkwancin masana’antar Nollywood, John Ikechukwu Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, ya taba rasa dansa Emmanuel Mandela mai shekara 2 a duniya a shekarar 2012.

An rawaito cewar Emmanuel ya rasu ne sakamakon ciwon hanta, ko da yake, Mista Ibu ya dora laifin sakacin asibiti a matsayin musabbabin mutuwar dansa.

4. Aisha Falode

Shahararriyar ‘yar jaridar kwallon kafa ta Najeriya kuma shugabar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya (NWFL), Aisha Falode, a 2014 ta bayyana rasuwar danta mai shekara 19 a duniya.

An rawaito cewar Toba Falode ya rasu ne sakamakon turo shi da aka yi daga bene mai hawa 17 a Dubai a wata makarantarsu, sai dai binciken ‘yan sanda ya ayyana lamarin a matsayin hatsari.

5. Eucharia-Anunobi Ekwu

Fitacciyar jarumar Najeriya da ta zama a 2017 ta rasa danta tilo, Raymond Ekwu, sakamakon kamuwa da ciwon amosanin jini.

Jarumar mai shekara 57, ta bayyana cewa likitan Raymond ne ya kashe mata da bisa kuskure, sai dai ba ta bayyana yadda lamarin ya faru ba.

6. Iya Rainbow

Wata fitacciyar jarumar fina-finai, mai suna Idowu Philips, wacce aka fi sani da Iya Rainbow, ta rasa ‘yarta, Sola Osborne tana da shekara 46.

A ranar 14 ga watan Janairu, 2016, Sola ta mutu sakamakon kamuwa da ciwon gyambon ciki saboda yawan azumin da take yi.

7. Ada Ameh

Aladi Ameh, diya ga jarumar fina-finan Nollywood, Ada Ameh ta rasu sakamakon tiyatar da aka yi mata sakamakon ciwon kwakwalwa da ta sha fama da shi.

Ada ta shiga damuwa kan mutuwar diyarta tilo kacal, wanda ita ma daga baya ta yi bankwana da duniya a watan Yulin 2022.

8. D’Banj

Mawakin Najeriya, Oladapo Daniel Oyebanjo, wanda aka fi sani da D’Banj, ya rasa dansa, Daniel Oyebanjo a watan Yunin 2018.

Rahotanni sun bayyana cewa yaron dan kimanin watanni 13 ya nutse a ruwa a gidansu na Ikoyi da ke Legas yayin da suka kai ziyara ga abokansu.

9. Davido

A wani labarin kuma, a ranar Litinin ce, shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya rasa dansa mai shekara uku a duniya, Ifeanyi Adeleke.

Rahotanni sun ce Ifeanyi ya nitse a cikin ruwa ne a gidansu da ke unguwar Banana Island a Legas, a lokacin da ‘yar gidan ke kula da shi.

Davido da Chioma suna kasar waje lokacin da lamarin ya faru.