✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitattun jaruman da rasuwarsu ta girgiza Kannywood a 2021

Ga wasu daga cikin jaruman da suka rasu a shekarar da muke bankwana da ita.

A shekarar 2021, masana’antar Kannywood ta dan farfado daga barcin da ta shiga a ’yan shekarun baya, musamman a bara da annobar CIVID-19 da tsayar da komai a duniya, ciki har da harkokin fim.

Sai dai a lokacin da masana’antar take kokarin farfadowa, wasu daga cikin manyan jarumanta sun rasu, kuma hakan ya jefa ta cikin jimami da rudu.

Ga wasu daga cikin jaruman da suka rasu a shekarar 2021 da muke bankwana da ita

Zainab Booth

A daren Alhamis, 1 ga Yulin bana ce tsohuwar fitacciyar jarumar Kannywood, Zainab Booth ta kwanta dama, sannan aka yi mata jana’iza a safiyar Juma’a.

Rasuwar tsohuwar jarumar ta jefa masana’antar cikin jimami, musamman kasancewar ta taka rawar gani sosai wajen ganin ci gaban masana’antar, sannan ’ya’yanta suka dora daga inda ta tsaya.

Marigayiyar, ita ce mahaifiya ga jarumai Maryam Booth da Ramadan Booth, wadanda suna cikin fitattun jaruman Kannywood da har yanzu tauraruwarsu ke haskawa, sai kuma kaninsu Amude Booth da shi ma ya taba harkar.

Tsohuwar jarumar ta rasu ne bayan jinyar da ta sha, ciki har da tiyatar kwakwalwa da aka yi mata.

Marigayiya Zainab Booth

Isiyaku Forest

Isiyaku Forest fitaccen mawaki ne a masana’antar Kannywood wanda mutane da yawa ba su san shi ba sai bayan rasuwarsa.

Marigayin, wanda ya fi fice a wakokin Jam’iyyar APC ne ya rera wakar nan da ake cewa, “Kara fada musu dai mu kasarmu APC muka yi, in za ai zabe a yi gaskiya ba za mu yarda da rinto ba, Najeriya sai Baba Buhari, gaskiya dokin karfe.”

Ya rasu ne a ranar 4 ga Satumba bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.

Ko a makon da ya rasu, ana shirye-shiryen fita da shi kasar waje ne, sai ya ce ga garinku nan.

Rasuwar Isiyaku ta matukar girgiza masana’antar, inda ko a watan jiya sai da fitaccen mawakin Shugaba Buhari, Malam Ibrahim Yala ya tuno da marigayin ta hanyar sanya hotonsa a shafinsa na Instagram, sannan ya masa addu’a.

Marigayi Isiyaku Forest

Ahmad Aliyu Tage

A ranar Litini, 13 ga Satumba ce fitaccen mai daukar hoto kuma jarumin barkwanci a masana’antar Kannywood, Ahmad Aliyu Tage ya rasu.

An a yi jana’izar marigayin ne a Unguwar Sabuwar Abuja da ke Karamar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano.

Marigayin ya rasu bayan gajeriyar jinya da ya yi.

Ana tuna shi da rawar da ya taka a fim din ‘Namamajo’ inda ya fito a matsayin mai tabin hankali duk abin da aka ce masa, sai ya amsa da ‘Sai bayan kwana biyu.”

Marigayi Ahmad Aliyu Tage

Alhaji Yusuf Barau

A ranar Laraba, 15 ga Satumban bana ce masana’antar Kannywood ta rasa daya daga cikin dattawan masana’antar, Alhaji Yusuf Barau.

Alhaji Yusuf yana cikin dattawan masana’antar da aka dade ana damawa da su.

Alhaji Yusuf Barau tsohon ma’aikacin Hukumar Wasanni da Al’adu ce ta Jihar Kaduna, ya rasu a garin Kakuri na cikin birnin Kaduna, sannan aka binne shi a Zariya.

Ya rasu yana da shekara 61, kuma ya bar mata daya da ’ya’ya takwas.

Marigayi Alhaji Yusuf Barau

Sani Garba SK

A ranar Laraba da 15 ga watan Disamba ce aka samu labarin rasuwar jarumin masana’antar Kanywood, Sani Garba SK, sannan aka yi masa jana’iza da safiyar Alhamis.

Rasuwar marigayin wanda ya sha fama da jinya na tsawon lokaci ta girgiza masana’antar matuka.

An sha yada jita-jitar marigayin ya rasu, kafin daga baya a gane ba haka ba ne.

A watan NUwamba ma, an yi jita-jitar, inda ya fito ya bayyana cewa idan lokaci ya yi ba sai an yi jita-jitar ba ma, zai rasu.

Daga cikin abubuwan da za a tuna marigayin akwai Fim din ‘Badali’ inda a cikin fim din ne marigayin yake cewa wani yaro “Za ka ci banana?” Da kuma inda yake cewa ‘Kar ka ba da ni mana Dumbadus’.

Wadannan kalmomi da ya yi amfani da su an dade ana kiransa da su.

Sai kuma fim din ‘Dabi’a’ da marigayin ya fito a matsayin mijin jaruma Hadiza Kabara, inda ya karo amarya sannan ya zo da niyyar ya hada su.

A nan aka yi wakar “Ya matana nasiha zan muku babba”.

A cikin wakar ce a karshe da ya nuna wa Hadiza Kabara alamar wariya da wulakancin cewa talaka ce, sai ta yi Larabci ta nuna musu cewa ilimin addini ya fi.

Marigayin ya fito a fim din ‘Gargada’ mai dogon zango da a yanzu haka ake haskawa a YouTube.

 

Marigayi Sani Garba SK

Wasu da suka rasu kuma sun hada da Shugaban Kungiyar Mawakan Kaduna, Malam Sani Maidangiwa, sai mahaifiyar Umar Gombe, wadda ita ma rasuwarta ta jefa masana’antar cikin jimami.