Gwamnonin jam’iyyar APC sun mika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sunan masu neman takara biyar don ya zabi daya daga ciki a matsayin dan takarar Shugaban Kasa na maslaha a jam’iyyar.
Wata majiya mai tushe ce ta tsegunta wa Aminiya hakan, inda ta ce Gwamnonin sun mika sunayen ne da sanyin safiyar Talata.
- Ya maka Hadiza Gaban a gaban kotu saboda ta ki auren shi
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Bindiga Suka Hallaka Mutane A Coci A Jihar Ondo
Sunayen, a cewar majiyar sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da na tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu da kuma na Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
Sauran su ne tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi
Tun da farko dai Gwamnonin sun tattauna da Buhari, inda suka yi alkawarin komawa Fadar Shugaban Kasa bayan sun tattauna da Kwamitin Zartarwar jam’iyyar na kasa.
“Su fitar da mutum daya daga yankin Kudu maso Gabas, daya daga Kudu maso Kudu, sai kuma uku daga Kudu maso Yamma, kammar yadda yake a matsayar da suka dauka cewa mulki ya koma Kudu,” inji majiyar.
Ya ce ana sa ran Shugaba Buhari ya dauki sunan mutum daya daga jerin sunayen.
A ranar Talata ce dai jam’iyyar za ta zabi wanda zai tsaya mata takarar a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.
A ranar Litinin ce dai Shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu ya ayyana sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, a matsayin dan takarar maslaha na jam’iyyar.
Sai dai daga bisani Fadar Shugaban Kasa ta nesanta kanta da sanarwar, inda ta ce Buharin bai zabi kowa a matsayin dan takara ba.
Ku ci gaba da kasancewa da Aminiya don kawo muku abubuwan da za su wakana a wajen zaben fitar da gwanin.