✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitacciyar mai karanta labaran NTA, Aisha Bello ta rasu

Aisha Bello ta shafe kusan shekara 20 tana karanta labarai a gidan talabijin na NTA.

Fitacciyar mai gabatar da labarai a gidan talabijin na Najeriya (NTA), Aisha Bello, ta rasu.

Aisha, wadda ta shahara a NTA ta rasu da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi.

Duk da yake har yanzu babu cikakken bayani game da rasuwarta, amma ta yi aiki har ta kai matsayin manaja a NTA, kuma ta yi ritaya a watan Mayun 2022.

Rahotanni sun bayyana cewar za a yi jana’izar ta a babban masallacin kasa da ke Abuja, a yau.

Marigayiyar ta yi aiki tare da fitattun mutane kamar Cyril Stober, Eugenia Abu da dai sauransu.

An fi sanin ta a matsayin daya daga cikin manyan masu karanta labaran NTA na karfe 9 na dare a shekaru 20 da suka gabata.

A cikin wata sanarwa da ’yan uwanta suka fitar, sun bayyana cewar, “Innalillahi wa inna ilai raji’un. Allah Ya gafarta wa Hajiya Aishat Bello Mustapha, mahaifiyarmu.

“Lallai ke mutuniyar kirki ce Mama, lallai kina da kirki. Za mu yi kewar ki da fatan Allah Ya gafarta miki.”

Za a yi jana’izar da karfe misalin karfe 1 na rana a ranar Litinin.