✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fitacciyar jarumar Nollywood, Adah Ameh, ta rasu

Jarumar ta yanke jiki ta fadi ne a wajen wani taro

Shaharariyyar jarumar barkwanci a masana’antar shirya fina-finan Kudancin Najeriya ta Nollywood, Ada Ameh, ta rasu.

Shugaban kungiyar jaruman Najeriya, Emeka Rollas, ya ce ta rasu ne a wani asibiti a jihar Delta a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli.

Ada Ameh ta rasu tana da shekara 48 a duniya.

An rawaito cewar ta kai ziyara wani babban kamfanin mai ne tare da iyalanta lokacin da ta fadi ba zato ba tsammani a yayin wani taro.

An garzaya da Ada zuwa asibiti inda aka tabbatar da rasuwarta.

A watan Oktoban 2020, jarumar ta Nollywood ta rasa danta daya tilo, kuma a watan Yunin 2022, ta bayyana cewa tana fama da ciwon matsananciyar damuwa.

Ameh, wacce ta taka rawar Anita a cikin fim din ‘Domitilla’ a shekarar 1996, ta shahara a bangaren barkwanci, musamman a cikin shirin ‘The Johnsons’ mai dogon zango.

Tuni jarumai ‘yan uwanta suka shiga mika sakon ta’aziyyarsu ga ‘yan uwa da iyalan mamaciyar.