✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitaccen masanin kimiyya Stephen Hawking ya rasu

A shekaran jiya Laraba ce  fitaccen masanin kimiyyar motsin abubuwa (Phisics) a duniya Farfesa Stephen Hawking ya rasu yana da shekara 76, inda ya rasu…

A shekaran jiya Laraba ce  fitaccen masanin kimiyyar motsin abubuwa (Phisics) a duniya Farfesa Stephen Hawking ya rasu yana da shekara 76, inda ya rasu a gidansa da ke garin Cambridge a safiyar ranar kamar yadda danginsa suka sanar.

Masanin kimiyyar dan kasar Birtaniya ya yi fice ne sakamakon aikace-aikacensa kan wani yanki da masana kimiyya ke hasashen cewa duk abin da ya gifta ta wurin zai bace.

Sannan ya rubuta litattafai da dama kan kimiyya ciki har da ‘A Brief History of Time’. Tun yana dan shekara 22 likitoci suka gano cewa yana fama da wani nau’in cuta wacce ke shafar kwakwalwa da kuma jijiya ‘motor neurone’. Cutar ta sa ba ya iya tafiya sai a keken guragu, sannan ba ya magana sai da taimakon na’ura.

A wata sanarwa da ’ya’yansa, Lucy da Robert da Tim suka fitar, sun ce: “Muna cikin matukar bakin cikin rasa mahainfinmu abin kaunarmu a yau. kwararren masanin kimiyya ne kuma gwarzo wanda rawar da ya taka za ta ci gaba da wanzuwa a doron kasa nan da shekaru masu tsawo.” 

Jama’a da dama na ci gaba nuna alhininsu kan rasuwar Farfesa Hawking. Firayi Ministar Birtaniya, Theresa May ta bayyana shi a matsayin ‘kwararre kuma gwarzo a cikin gogaggun masana kimiyya na wannan zamani.’

An haifi Farfesa Stephen Hawking ne a ranar 8 ga Janairun 1942 a Odford da ke kasar Ingila. Ya shiga Jami’ar Odford ne domin karanta kimiyya a 1959, daga bisani ya yi digiri na uku a Jami’ar Cambridge. An gano yana da cutar motor neurone a 1963, inda likitoci suka ce rayuwarsa za ta kare bayan shekara biyu. Ya zama farfesan lissafi a Jami’ar Cambridge a  1979.

Ya wallafa shahararren littafin nan ‘A Brief History of Time’ a 1988, wanda aka sayar da sama da kwafi miliyan goma a sassan duniya. Ya taba watsi da lambar girmamawa saboda nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnati ke daukar nauyin ilimin kimiyya.