Fitaccen ɗan kasuwar nan na Jihar Kebbi, Alhaji Balanbala Jega wanda aka fi sani da BLB, ya rasu.
Ya rasu a ranar Lahadi yana da shekara 54 a duniya.
- Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu
- Zargin Kwartanci: Allah Zai bi min haƙƙina a lahira — Wanda yake ƙara
Margayin ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, kuma ya rasu ya bar ’ya’ya 21 da mata huɗu.
Margayin ya kasance shugaban rukunin manyan shaguna (BLB Super Market) da ke garin Jega da Birnin Kebbi.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ziyarci garin Jega, inda ya yi ta’aziyar rasuwar margayin a ranar Litinin.
Ya bayyana rasuwar ɗan kasuwar a matsayin babban rashi ga jihar.
Sarkin Kabin Jega, Alhaji Arzika Muhammad Bawa ne, ya karɓi tawagar gwamnan a madadin iyalan margayin a lokacin ziyarar ta’aziyar.
Sheikh Abbas Jega, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da ’yan uwan mamacin.
“Alhaji Bala mutum ne, dattijo na haƙiƙa, mutum ne mai haƙuri da sanyin hali.
“Muna roƙon Allah Ya sanya Aljanna Firdaus ta zama makoma gare shi da sauran magabatanmu gaba ɗaya.”
Honarabul Mansur Musa Jega, shi ma ya miƙa ta’aziyarsa ga iyalan mamacin.
“Ina miƙa saƙon ta’aziyyar wannan babban rashi ga iyalan mamacin, ’yan uwa da kuma al’ummar ƙaramar hukumar Jega.
“Cikin alhini nake jajanta wa al’ummar Jega game da rasuwar Alhaji Balan Bala Jega, Shugaban Rukunin BLB Super Market.
“Rasuwarsa babban rashi ga jama’ar garin Jega da ma Jihar Kebbi baki ɗaya.”