Hukumar gidan waya ta kasa (NIPOST) ta zargi takwararta ta Tattara Haraji ta Kasa (FIRS) da yin karya kan asusun harajin kan sarki na hukumar da ke Babban Bankin Kasa (CBN).
Babban manajan yada labarai na NIPOST, Franklin Alao ya ce hukumar ta bude asusunta ne da CBN saboda harajin kuma sun bi ka’ida wajen budewa.
Franklin ya ce, “NIPOST ta samu labarin wani zargi da FIRS ta yi cewa NIPOST ta kirkiri wani asusun harajin kan sarki ba bisa ka’ida ba.
“Muna so jama’a da su fahimci cewa babu kanshin gaskiya a zarge-zargen, hasali ma an yi su ne domin kawar da hankulanasu daga hakikanin abun da yake faruwa”, inji shi.
Ya ce CBN ne ya bude asusun da hukumar ta ke ikirarin an bude ba bisa ka’ida ba karkashin tsarin Asusun Ajiya na Bai Daya (TSA) bayan tattaunawa tare da samun amincewar Babban Akanta na Tarayya.
Ya kara a cewa NIPOST ta fara amfani da asusun ne lokacin da CBN ya umarci bankunan kasuwanci su fara cirar N50 daga asusun ajiyar jama’a a matsayin harajin na kan sarki.
“Duk kudaden da aka zuba a asusun mallakin kasa ne kuma NIPOST ba ta da damar taba ko sisi a ciki, saboda haka maganar an bude shi ba bisa ka’ida ba ko za a yi facaka da shi ba ta taso ba”, inji jami’in.