Hukumar gasar Firimiyar Ingila ta tsige Roman Abramovich daga shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea biyo bayan takunkuman da gwamnatin Birtaniya ta kakaba masa.
Haka kuma, a ranar Asabar kamfanin kera motoci na Hyundai da ke daya daga cikin masu daukar nauyin kungiyar ya dakatar da yarjejeniyarsa da kungiyar.
- Mustafa Shehu: Mutumin Kano da ya zama Shugaban Kungiyar Injiniyoyi ta Duniya
- Ban fita daga PDP ba tukunna —Kwankwaso
A matsayin martani ga mamayar Ukraine da Rasha ta yi, gwamnatin Birtaniya ta rike kadarorin Abramovich da ke Birtaniya a ranar Alhamis, matakin da ya sa dole attajirin ya dakatar da sayar da kungiyar kamar yadda ya kudirta tun da farko.
Wasu bayanai sun ce a yanzu bayan tattaunawa da mahukuntan kungiyar suka yi da wakilan gwamnatin Birtaniya, ana iya sayar da kungiyar ba tare da Abramovic ya samu ko sule ba.
Hukumar gasar Firimiyar Ingilar ta ce tsige Abramovich ba zai yi tasiri a harkokin kungiyar ba, musamman wajen atisaye da buga wasannin gasar Firimiya.
Wannna matakin dai zai bijiro da batun sayar da hannayen jarin kungiyar, abin da Abramovich ya yi yunkurin yi tun da farko a ranar 2 ga watan Maris, bayan da majalisar dokokin Birtaniya ta fara barazanar kakaba masa takunkumi.