A yau Juma’a ake sa ran Firayi Ministan Iraki Adel Abdel Mahdi zai mika takardar murabus ga Majalisar Dokokin Kasar sa’o’i bayan jagoran mabiya Shi’a ya yi kira a janye goyon bayan da ake ba shi a majalisar, yayin da zanga-zanga ta yi kamari a kasar. A waje guda rahotanni na cewa yawan mutanen da aka kashe a garin Nasiriyya zuwa shekaranjiya Laraba sun kai 15.
Bayan mutane da dama sun mutu a zanga – zangar da ke ci gaba da rincabewa, jagoran Shi’a, Ayatollahi Ali Sistani ya bukaci illahirin ’yan majalisar zartarwar su yi murabus, yana mai kiran a janye goyon bayan da ake ba su.
A hudubarsa ta Juma’ar makon jiya, Ali Sistani ya caccaki yadda al’amura suka ci gaba da yamutsewa a kasar.
Sa’o’i bayan wannan kira da jagoran Shi’ar ya yi ne, Firayi Minista Adel Abdel Mahdi ya bayyana niyyarsa ta mutunta bukatun al’ummar kasar da na jagoran addinin, bayan kusan wata biyu ana mummunar zanga-zanga da ta ci rayuka 400.
Wannan bayani na Mahdi ya kasance wani babban albishir ga dimbim masu zanga -zanga da suka taru a Dandalin Tahrir don yin tir tare da nuna kin jinin gwamnatin da suke wa kallon gwana wajen rashawa, baya ga rashin sanin makamar aiki, inda suka buge da kade-kade da bushe-bushe.