Jim kadan bayan Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi murabus daga mulkin kasar, shi ma Firay Ministan Habasha (Ethiopia) Hailermarian Desalegn ya yi murabus daga bakin aiki.
Gidan talabijin na kasar ne ya fitar da sanarwar cewa Firay Minista Hailermarian Desalegn din ya yi murabus.
Har zuwa yanzu dai ba a samu sahihin dalilin da ya sa ya yi murabus din ba.