✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Firaiministan Italiya Giuseppe Conte ya yi murabus

Firaiministan Italiya, Giuseppe Conte, ya gabatar wa da Shugaban Kasa Sergio Mattarella wasikarsa ta murabus a ranar Talata. Wannan na zuwa ne a yayin da…

Firaiministan Italiya, Giuseppe Conte, ya gabatar wa da Shugaban Kasa Sergio Mattarella wasikarsa ta murabus a ranar Talata.

Wannan na zuwa ne a yayin da Firaiministan ke fatan samun damar kirkirar wata sabuwar Gwamnati da kuma sake neman samun rinjayen Sanatocin da za su mara masa baya a Majalisar Dokokin Kasar.

A makon da ya gabata ne mafi rinjayen ’yan Majalisar Dattawan Kasar suka dawo daga rakiyar Firaiminista Conte bayan tsohon Firaminista Matteo Renzi ya juya masa baya inda ya bayyana bacin ransa a kan Gwamnatin Kasar dangane da rikon da ta yi wa annobar Coronavirus da kuma matsin tattalin arziki.

Sai dai Conte ya yi kicibus da rashin sa’a a yayin da galibin Sanatocin jam’iyyar Centrist da Independent wadanda ya nemi hadin kansu suka ki amincewa da bukatarsa ta maye babban gurbin da Firaiminista Renzi ya bari.

Wannan rashin zabi da ya fuskanta ya sanya ya yi murabus babu shiri kuma ya nemi kawo hargitsin siyasa a gwamnatin kasar da nufin samun wadataccen lokacin da zai kawo karshen matsalarsa ta hanyar kulla yarjejeniya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, ana sa ran Shugaba Sergio zai amince da murabus din sannan kuma ya shiga tuntubar shawarwarin shugabannin manyan jam’iyyun kasar domin samun tabbaci a kan matsayarsu.

Idan yana tunanin Firaiminista Conte zai cimma manufarsa ta samun magoya bayan da suka dace wajen kafa sabuwar gwamnati, zai bashi dama ta kwanakin kalilin domin kammala yarjejeniyar sannan ya kafa sabbin ’yan majalisar ministoci.

Idan kuma lamarin ya faskara, Conte ya yi gumin hanci a banza, dole ne Shugaba Sergio ya yi kiran a yi zabe shekaru biyu kafin wa’adin gudanarsa.

Rikicin siyasa na kara ta’azzara ne a sakamakon yadda annobar Coronavirus ta salwantar da rayukan fiye da ’yan kasar Italiya 85,000.

Alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya sun nuna cewa Italiya ce kasa ta biyu a nahiyyar Turai bayan Birtaniya, kuma kasa ta shida a duniya wacce annobar Coronavirus ta fi kashe al’ummarta.

Wanan lamari ya jefa kasar cikin matsin tattalin arzikin da bata taba fuskanta ba tun bayan Yakin Duniya na biyu a yayin da gwamnatin kasar ke fafutikar shimfida tsare-tsare mafi dace wajen kashe Dala biliyan 240 daga Asusun Kungiyar Tarayyar Turai domin tayar da komadar tattalin arzikinta.