✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fintiri ya nada sabbin sarakuna 7 a Adamawa

Gwamna Ahmad Fintiri na Jihar Adamawa ya amince da naɗin sababbin sarakuna da hakumai bakwai

Gwamna Ahmad Fintiri na Jihar Adamawa ya amince da naɗin sabbin sarakuna da hakimai bakwai a masarautun Jihar.

Nadin sabbin sarakunan aka zaɓo ya fara aiki ne nan take, kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.

Sabbin sarakunan su ne Alhaji Sani Ahmadu Ribadu a matsayin Sarkin Fufore, da Ahmadu Saibaru a matsayin Sarkin Maiha, da Barista Barrister Alheri B. Nyako a matsayin Tol Huba da Farfesa Bulus Luka Gadiga a matsayin Mbege Ka Michika.

Sauran su ne Dakta Ali Danburam a matsayin Ptil Madagali, da Aggrey Ali a matsayin Kumun Gombi, da John Dio a matsayin Gubo Yungur.

Gwamnan ya bayyana cewa an zaɓo su ne bisa cancanta da farin jininsu, tare da taya su murna game da sababbin matsayin da suka samu.

Ya buƙace su da kasance masu gaskiya da riƙon amana da adalci wajen gudanar da ayyukansu.