✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ɗauki mataki ne domin kawo sauye-sauye a ɓangaren sarautar gargajiya a jihar.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ƙirƙirio sabbin masarautu guda bakwai don sauya tsarin sarautar gargajiya da kuma inganta zaman lafiya da ci gaba a jihar.

Sabbin masarautun sun haɗa da Huba (Hong), Madagali (Gulak), Michika (Michika), Fufore (Fufore), Gombi (Gombi), Yungur (Dumne), da Maiha (Maiha).

Huba, Madagali, Michika, da Fufore an ba su matsayin na biyu, yayin da Gombi, Yungur, da Maiha suka samu matsayin na uku.

Gwamnan, ya ce wannan mataki na da nufin inganta shugabanci, magance rigingimu, da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’ummomi daban-daban.

Har ila yau, ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.

Fintiri, ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a shekarar 2024, ciki har da ci gaba a fannin gine-gine, tsaro, da saka hannun jari a ɓangaren walwalar jama’a.

Ya kuma tabbatarwa da jama’a cewa zai ci gaba da aiki tuƙuru wajen cika alƙawarin da ya yi musu.

Ya yi fatan samun haɗin kai don samun ƙarin nasarori a shekarar 2025.