✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fim ɗin ‘Ƙanwata ce’ yana koyar da yadda ake kare haƙƙin ƙanne mata ne — Yaron Malam

Balarabe Musa Aminu fitaccen tauraron finafinan Hausa ne a masana’antar Kannywood, wanda fim din “A Duniya” ya fito da shi, ya haskaka shi, inda mafi…

Balarabe Musa Aminu fitaccen tauraron finafinan Hausa ne a masana’antar Kannywood, wanda fim din “A Duniya” ya fito da shi, ya haskaka shi, inda mafi yawa an fi sanin Balarabe Musa Aminu da sunan Yaron Malam.

A zantawarsa da Aminiya ya bayyana wa wakilinmu cewa, ya fara shirya nasa fim din mai suna “Ƙanwata ce”.

Har ila lau, Yaron Malam ya bayyana wa Aminiya yadda fim din nasa ya samo suna, inda ya ce kara ce ya yi wa wata ƙanwarsa.

Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

Aminiya: Wanne ƙarin bayani za ka yi mana dangane da ci gaban da Kannywood ta samu a yanzu?

Balarabe Musa: Alhamdulillahi ni dai da farko koya min yadda ake yin fim aka yi, amma Alhamdulillahi yanzu saboda irin yadda na dauki abin da nake yi da mahimmanci har ga shi Allah Ya taimake ni, yanzu na zo ina yin nawa fim na kaina .

Kuma ai ka san ƙalubale a rayuwa kowa yana fuskantarsa. Amma ni yanzu ƙalubalen da nake samu shi ne na rashin iya abin sosai kamar yadda wadanda suka dace a harkar ke yi, don ni kawai a da dan ƙasa ne kamar sauran taurari da ake gayyatowa, a ba su abin da ake so su yi, a biya su. Amma yanzu ta kai ga ina shirya nawa fim din mai suna “Ƙanwata ce”, kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu, domin yanzu mutane da dama suna amfana da saƙon.

Aminiya: Kana nufin fim din A duniya da ka yi a nan ne ka samu gogewa da kuma ƙwarewa?

Balarabe Musa: Gaskiya dai ta sanadiyar fim din A duniya na ƙara samun basira da kuma gogewa. In aka yi la’akari da irin yadda mutane suke kira na don in yi musu aiki da kuma irin yadda ni ma na zama mai bayar da umarni, wanda na koya a lokaci da ake daukar fim din ‘A duniya’. Na sa himma, ina kula da yadda ake yi, wato yadda shi Daraktan yake bayar da umarni da kuma yadda shi mai shirin fim din, wato Tijjani Asase yake gudanar da abubuwansa da yadda yake aiki da ƙwaƙwalwa da sauran harkoki na yadda ake yin fim din. Ta haka ne Allah Ya taimake ni, na koya. Haka kuma, gaskiya ce babu wani fim da ya fito da ni kamar fim din ‘A Duniya’, inda yanzu ni ma Alhamdulillahi babu abin da zan ce wa Allah sai dai godiya game da yadda nake tafiyar da harkata.

Aminiya: Wato dai za a iya cewa Tijjani Asase ne ubangidanka?

Balarabe Musa: Eh, haka ne babu abin da zan ce sai godiya ga Allah da kuma godiya ga maigidana Tijjani Asase domin shi ya yi min koma a harkar fim, musamman fim din ‘A Duniya’ da ya sa ni kuma ya ba ni cikakkiyar dama.

Aminiya: Yau ga shi kai ma wuyanka ya yi kauri, ka fara shirya naka fim din mai suna ‘Ƙanwata ce’. Me ya sa ka yanke shawarar sa wa fim din suna ‘ƙanwata ce’ kuma wane tasiri hakan ke da shi?

Balarabe Musa: To shi fim din ƙanwata ce ya samo asali ne tun a gidanmu. A gida ina da wata ƙanwa mai suna Fauziyya. Idan na shigo gida, tana ce min yayana, ni kuma ina ce

mata ƙanwata, wanda kuma sanadiyar irin yadda nake yin haba-haba da ita a gida kuma da yadda nake kare ta in ta yi wa Babarmu laifin da za ta hukunta ta shi ne za a ga raina yana ɓaci, sai ta rugo a guje wurina. Ko kuma idan ta san ta yi laifin da za a hukunta sai ta rugo wurina. Sannan idan tana da wata buƙata wurina take zuwa ta fada min saboda irin shaƙuwar da ke tsakaninmu.

Don haka na yi nazarin ta wacce hanya zan karrama ta, sai na sanya wa sunan fim dina ƙanwata ce domin ita ma ta yi farin ciki.

Aminiya: Shi wane darasi fim din ƙanwata ce yake koyar da al’umma, musamman wadanda suka kalli fim din?

Balarabe Musa: Fim din ya ƙunshi rayuwa ce a tsakanin ’yan’uwa, musamman ƙanne mata, inda a ciki ana nuna kulawa da su da nuna musu so ta yadda aka nuna yadda na nuna rashin son duk wani abu da zai sosa mata rai. Wannan shi ya sa idan ka kalli fim din za ka ga a sanadiyyar kare muradanta za ka ga na riƙa shan wahala, amma hakan bai sa na daina kare muradunta ba.

Aminiya: Me za ka ce dangane da yadda yawanci yanzu masu yin fim suka koma dora finafinansu a Yourube Channel maimakon yi a kaset ko nunawa a sinima?

Balarabe Musa: Ka san ana yin kasuwanci ne don riba. Ka ga haka zamani ya zo da shi. Yanzu a intanet ne musamman a YouTube za ka saka fim, a kalla, kuma su biya ka. Ai a baya ba haka ake yi ba, amma yanzu ci gaban da aka samu, shi ya sa kake ganin kowa

yake dora fim dinsa a Youtube . Ni ina fim ne saboda abu biyu. Na farko na dauke shi a matsayin sana’a. Sannan na biyu kuma na dauke shi a matsayin wata hanya ta sama wa mutane aikin yi. Ka ga yanzu mutane dadama suna cin abinci a ƙarƙashina. Don haka na san duk wanda Allah Ya sa ya samu hanyar da zai ci abinci ta hannunka, to kuwa Allah zai ba ka lada. To ka ga ko a masu taya ni aiki akwai mutane da yawa. Misali, akwai mai daukar bidiyo, akwai mai daukar murya, akwai mai kula da ci gaban shirin da sauran masu ayyuka daban-daban da nake aiki da su. Haka kuma duk wanda ya zo ko ka dauko shi haya, dole za ka biya shi kudin aikin da yake yi maka . To wannan ma yana ƙara min jin dadi saboda samun walwala da nake ganin wasu na yi ta hanyata

Aminiya: Me za ka ce dangane da yanayi na sauyi na rayuwa da kowa yanzu yake ji. Shin ko abin ya shafi sana’arka a matsayinka na mai shirya fim?

Balarabe Musa: Eh Alhamdulillahi, a gaskiya akwai ƙalubale da yawa, musamman na rashin kudi da kuma tsadar kaya. Amma gaskiya wannan ba ta sa mun fasa shirya fim ba. Tun da na fara daukar wannan fim din na ƙanwata ce, gaskiyar magana kamar yadda na gaya maka Alhamdulillahi duk wadanda muke tare da su, ina ƙoƙarin faranta musu rai ta hanyar biyan su haƙƙinsu. Kuma su ma suna nasu ƙoƙarin don su faranta min. Don ka san ita rayuwa yanzu da kake gani komai taimake ni, in taimake ka ne. Don haka a gaskiya babu matsala.

Ka ga yanzu haka maganar nan da muke yi da kai, ina Ilori a Jihar Kwara,

inda na zo don aikin daukar fim. Daga Ilori kuma zan tafi Ibadan zuwa garin Badun, daga can kuma Yobe na hara. A haka dai ake samu ana warwarewa

Aminiya: Wadanne irin ƙalubale kake fuskanta a yanzu?

Balarabe Musa: Babban ƙalubalen da nafara samu shi ne na wurin iyayen gidana da kuma wadanda nake tare da su. Ƙalubalen dana samu awurin iyayen gidana su ne akwai wasu maganganu da suke fitowa na rabuwar kai tsakanin iyayen gidana kamar kamafinmu na A Duniya. Domin duk duniya ba ni da wurin da nake alfahari da shi kamar fim din A Duniya, ba ma ni kadai ba gaskiya, duk wanda yake cikin fim din ya samu ƙalubale saboda kowannemu ba ya jin dadin abin da yake faruwa a tsakanin shugabanninmu.

Aminiya: Shi wancan ƙalubale da kake magana a kai mene ne yake jawo shi, hassada ce ko kuwa ya abin yake?

Balarabe Musa: Gaskiya dai kowa da yadda yake kallon abin. Amma ni akwai fuskar da nake kallon abun, amma ina addu’a Allah Ya kawo daidaituwar lamarin, kawunanmu su hadu, a zo, a ci gaba da tafiya kamar yadda ake yi a da

Aminiya: A iya cewa fim din ƙanwata ce da ka shirya ne ya fito da kai ?

Balarabe Musa: To gaskiya fim din ƙanwata ce ya ƙara min ƙaimi a harkar fim, kuma ni yanzu ma na fara harkar fim din da ko milyan nawa nake da ita zan iya kashewa, in yi fim don na san ba zan yi zan yi asararta ba. Bakin gwargwado na san harkar fim. Kuma zan iya cewa yanzu fim sana’a ta ce da take rufa min asiri.