✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

FIFA ta kara adadin ’yan wasan da za su buga wa kasashe a Qatar

Gasar ta wannan karon ta zo a wani yanayi da za ta ci karo da wasannin lig-lig na Turai.

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta amince da kara yawan adadin ’yan wasan da kowacce tawaga za ta kai Qatar yayin wasannin gasar Cin Kofin Duniya zuwa mutum 26, maimakon 22 da aka saba tsawon shekaru.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito sanarwar da FIFA ta fitar na cewa mafi karanci na adadin ’yan wasan da kowacce kasa za ta kai gasar shi ne 23 ko kuma mafi kololuwa 26.

FIFA ta ce matakin kara yawan ’yan wasan na da nasaba da yadda gasar ta wannan karon ta zo a wani yanayi da za ta ci karo da wasannin lig-lig na Turai wanda zai haddasa matsala ga kakar wasan da muke shirin shiga.

Gasar Cin Kofin Duniyar da za ta gudana a Qatar za ta fara ne daga ranar 21 ga watan Nuwamba a kuma kammala ta a ranar 18 ga watan Disamba.

Ko a gasar Euro 2020 da ta gudana a bara UEFA ta dauki makamancin wannan mataki na kara yawan ’yan wasan saboda yadda gasar ta zo dai dai lokacin da kungiyoyin turai ke tsaka da wasanninsu.

Tun daga shekarar 2002 ne yayin gasar Cin Kofin Duniya a Japan da Korea ta kudu FIFA ta kayyade amfani da yawan ’yan wasa 23.