✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

FIFA ta dakatar da Indiya daga harkar kwallon kafa

Hukumar AIFF tana cikin wani yanayi na rudani a karkashin kulawar masu jagorancinta.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta dakatar da Indiya daga shiga harkar kwallon kafa nan take har sai abin da hali yayi.

FIFA ta ce ta dauki matakin dakatar da Hukumar Kwallon Kafar Indiya (AIFF) a ranar Litinin, lura da karan tsaye da katsalandan da ake yi wa dokokinta a kasar.

Hakan na nufin FIFA ta kwace damar da ta ba wa Indiya ta karbar bakuncin gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ’yan kasa da shekaru 17, wadda aka shirya gudanarwa cikin watan Oktoba.

A halin da ake ciki dai hukumar ta AIFF tana cikin wani yanayi na rudani a karkashin kulawar masu jagorancinta.

Wannan dai na faruwa ne tun bayan da tsohon shugaban AIFF, Praful Patel ya zarce shekaru 12 na mafi tsawon wa’adin zama a kujerar shugabanci ba tare da an gudanar da sabon zabe, wanda kotu ta tabbatar da hakan ya saba wa ka’ida.

Patel, wanda ya rike manyan mukamai na gwamnati hade da mukaminsa na AIFF, ya jagoranci Hukumar Kwallon Kafar ta Indiya tun daga shekarar 2009, kuma ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Kungiyar Kwallon Kafa ta Jamus (DFB) a shekarar 2019.

A ranar 28 ga watan Agusta ne za a gudanar da sabon zabe wanda an soma sharar fage tun a makon da ya gabata, bayan da Kotun Kolin Indiya ta amince da wani lokaci da masu gudanar da zaben suka shirya.