✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

FGC Yauri: Dalibi ya rasu yayin artabun sojoji da ’yan bindiga

An ceto dalibai hudu da malami daya yayin artabun.

Daya daga cikin daliban Kwalejin Tarayya ta garin Yauri a Jihar Kebbi ya rasa ransa yayin artabu tsakanin sojoji da ’yan bindiga.

Mataimakin kwamandan rundunar hadin gwiwa a shiyyar Arewa maso Yamma, Air Commodore Abubakar AbdulKadir ne ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida a jihar ta Zamfara ranar Juma’a.

  1. ‘’Yan sanda sun sako ’yan bindigar da aka kama a Zariya’
  2. Matawalle ya dakatar da hukumar ZAROTA

Ya ce, “A safiyar yau, ’yan bindigar sun yi kacibus da mu a inda muka tare hanya, kuma nan take muka yi musu dirar mikiya.

“A yayin artabun ne suka saki dalibai biyar da malami daya, amma ina tunanin dalibi daya ya rasa ransa,” cewar Abdulkadir.

Ya kuma tabbatar da ceto dalibai hudu da malami daya yayin artabun da ya faru tsakanin rundunar sojin da ’yan bindigar.