Kwalejin Ilimin Kimiyya Ta Tarayya da ke Bichi a Jihar Kano, ta sanar da ranar Litinin 2 ga watan Nuwamba, a matsayin ranar koma wa domin ci gaba da dukkanin harkokinta na gudanarwa.
Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da magatakardar Kwalejin Alhaji Abdulkarim Bello ya fitar a ranar Talata.
- FCE Kano ta sanar da ranar komawa makaranta
- Makarantun kudi a Kano za su samu tallafin COVID-19
- Yadda yara a Kano ke damun iyaye kan komawa makaranta
Sanarwar ta ce an kammala duk wani shiri na kiyaye matakan da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta tanadar domin kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus.
“Hukumar Gudanarwar Kwalejin ta kafa doka tun daga kan ma’aikata, dalibai da masu kawo ziyara cewa za su ke amfani da takunkumin rufe fuska, da amfani da sinadarin tsaftace hannu (hand sanitizer), sannan kuma a rika bayar da tazara kamar yadda Mahukuntan Lafiya suka tanada”, cewar jawabin.
Ya kara da cewa, a duk lokacin da dalibai suka ji yanayi na rashin lafiya musamman wanda ya ke da alaka da cutar Coronavirus, su hanzarta zuwa asibitin Kwalejin domin bincikar lafiyarsu.
Bisa umarnin da Gwamnatin Najeriya ta bayar, tun a ranar 23 ga watan Maris na 2020, aka rufe Kwalejin ta FCE Bichi sakamakon barkewar annobar COVID-19.