Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta FBI sun kai samame a wani katafaren gidansa da ke bakin teku a Jihar Florida, yana mai siffanta lamarin a matsayin rashin da’a.
Sai dai Trump wanda ba ya cikin gidan a ranar Litinin da daddare, a cikin sanarwar da ya fitar ya gaza fadin dalilin da ya sa jami’an suka ziyarci gidansa suka kaddamar da bincike.
- Amurka na zawarcin hulda ta gaskiya da nahiyar Afirka —Blinken
- ‘Akwai ’yan kabilar Kanuri sama da miliyan 2 a Kano’
Sai dai wani dan tsohon shugaban, Eric Trump ya shaida wa tashar talabijin ta Fox News cewa, binciken da aka gudanar a gidan mahaifin nasa da ke Mar-a-Lago na da alaka da wasu takardu da ofishin adana takardun tarihi na Amurka ke nema ne.
Jaridar New York Times ta ambato tsohon shugaban na zargin ‘yan siyasar jam’iyya mai mulki ta Democrat da tura masa jami’an FBI domin su bankado wani abu da zummar goga masa kashin kaji, ya samu matsala, a takarar shugabancin Amurka da yake honkoro a shekara ta 2024.
Ita dai hukumar ta FBI ta kauce wa yin karin haske a kan samamen kamar yadda jaridar ta ruwaito.
Wasu majiyoyi a Amurka na cewa kotu ce ta sahale wa FBI din kutsa wa gidan Donald Trump domin bincike ko ya boye wasu takardun sirri na gwamnati.
A watan Fabrairun da ya gabata rahotanni sun ce an gano akwatuna 15 makare da muhimman takardun gwamnati da Trump ya wuce da su gidansa maimakon ya bar su a Fadar White House.