Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce faɗuwar da yaran da ake tuhuma a kotu suka yi wasan kwaikwayo ne, domin jan hankalin mutane.
Wannan dai na zuwa ne bayan gurfanar da ƙananan yara da manya da aka kama yayin zanga-zangar #EndBadGovernance da aka yi daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
- Neman belin N10m daga wurin ƙananan yara wauta ce — Kwankwaso
- Kashe Kwamred Bala Shugaban Cibiyar Horar da Naƙasassu ta Abuja ya ta da hankali
Yara huɗu daga cikin masu zanga-zangar sun yanke jiki sun faɗi a kotu, wanda hakan ya sa aka garzaya da su asibiti.
Amma Egbetokun, ya ce faɗuwar yaran ba komai ne face wasan kwsi5 don jan hankalin mutane.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya sanya wa hannu, Egbetokun ya ce rundunar tana sane da dokokin ƙasa da ke kan kowace mutum.
Ya bayyana cewa tuhume-tuhumen da ake zargin masu zanga-zangar sun haɗa da lalata kadarorin jama’a da kuma barazana ga tsaron ƙasa.
Sufeto ya yi kira ga jama’a da su yi adalci game da shari’ar da ake yi wa yaran, inda ya yi alƙawarin cewa za a gudanar da shari’ar bisa gaskiya da adalci.
“Yau, wani lamari ya faru a kotu, inda wasu yara shida daga cikin waɗanda ake zargi suka dinga faɗuwa, wanda hakan ya jawo hankalin kafofin yaɗa labarai kuma sun tsara hakan ne don cimma wata manufa,” in ji Egbetokun.
“Yaran da suka faɗi a kotun an ba su taimakon gaggawa, wanda hakan ya nuna yadda ’yan sanda suka damu da lafiyar duk waɗanda ke hannunmu, komai girman tuhumar da ake musu.”
Egbetokun ya ƙara tabbatar wa da jama’a cewa ’yan sanda suna aiki da adalci.
Kazalika, ya jaddada cewar suna kula da lafiyar waɗanda ake tuhuma da kuma kare haƙƙoƙinsu.