Kotu ta yanke wa wani fasto daurin shekara 21 a gidan yari bayan ta kama shi da laifin yi wa agolarsa mai shekara 10 fyade.
Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom ta yanke wa faston mai suna Anwana Peter Essien hukuncin ne bayan ya yi ikirari a gaban alkali cewa ya yi wa karamar yarinyar fyade da karfin tuwo a gidansa.
- Kotu ta tura Alhassan Doguwa gidan yari
- Gobara ta kone shaguna 80 a Kasuwar Kurmi
- EFCC ta gurfanar da A.A Zaura a Kano
A lokacin da ake gurfanar da shi a gaban kotun, faston mai shekara 37 ya bayyana wa alkali cewa da tsakar dare ne ‘shaidan’ ne ya sa shi aikata hakan a lokacin da yarinyar, wadda ke aji da na karamar sakandare.
Ya ce, “Sai da na ba ta abinci sannan na umarce ta da ta tube kayanta, amma ta ki. Shi ne na tilasta mata tubewa na kuma yi lalata da ita.”
Daga nan alkalin kotun, Okon Okon, ya ce, “Ikirarin yi fyade ga agolarsa da wanda ake tuhuma ya yi ta tabbatar da laifinsa.’’
Daga nan ya yanke wa Anwana Essien hukuncin daurin shekara 21 a gidan yari, kuma lissafin zai fara ne daga lokacin da faston ya fara zaman wakafi a gidan yarin Uyo.