Wani fasto ya kwace matar abokinsa da ƙudinsa Naira miliyan 105.
Ana zargin faston wanda yanzu yake hannun ’yan sanda a Legas, ya yi wa abokinsa da ke zaune a ƙasar Amurka tsafi ne ya karɓe masa kudi Naira 105 a hannunsa ta hanyar yaudara.
- Kannywood: Sunusi 442, Maryam Jankunne sun zama mashawartan Abba
- Gwamnati ta janye karar da ta shigar da ’yan kwadago
’Yan sanda sun ce faston ya haɗa baki da matarsa wajen damfarar abokin nasa bayan ya yi masa tsafi, daga bisani ya ƙwace matar abokin nasa da ’ya’yansu uku da motoci biyar da gidaje na tsawon shekaru 10.
Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sandan mai kula da shiyya ta biyu, ya sanar cewa faston ya shaida wa masu bincike cewa tsaface abokin nasa da ke zaune a Amurka ya yi wajen kwace iyalinsa da kudinsa Naira miliyan 105 da kuma gidaje a wurare daban-daban a Legas.
A cewarsa, ta hanyar tsafin ya sa abokin nasa sauya sunayen da ke kan takardun kadarorin da na ’ya’yansa zuwa na faston.
Mohammed ya ce matar faston ta shiga hannu, kuma ’yan sanda na farautar sauran masu hannu a badaƙalar, amma an cafke mutum biyar daga cikinsu.
Ya ce matar faston ta amsa cewa ita ce ta sauya takardar haihuwar ’ya’yan mutumin zuwa na mijinta, kuma ta karɓi Dala 17,000 daga hannun mutumin.
Jami’in ’yan sandan ya ce sai bayan shekara 10 abokin faston ya farga, inda ya dawo Najeriya ya kai ƙorafi.
Da farko faston ya shaida wa abokin nasa cewa wahayi ya samu ana umartarsa ya aikata hakan.
An ƙwato gidade da dama daga hannunsu, da kuma motoci uku, ciki har da Toyota Venza 2009, bas kirar Ashok Leland da sauransu.