✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasinjoji sun lakada wa ma’aikatan jirgin sama duka a Legas

An farfasa kwamfuoci aka lakada wa wasu ma'aikaan jirin sama duka saboda bacin rai

Majiyoyi a filin jirgin sun ce wasu fasinjojin sun makale a filin jirgin na sama da sa’o’i 24 bayan da aka dage tashin jirginsu da farko, daga karshe kuma aka soke.

Wani jami’i a filin jirgin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce “Wasu daga cikin fasinjojin tun jiya (Lahadi) suke jira bayan da aka dage tashin jirginsu.

“An yi musu alkawari cewa jirginsu zai tashi yau (Litinin) amma bayan jinkirin da aka samu na sa’o’i uku, sai aka ce an soke tashin jirgin.”

Hakan ne ya sa fasinjojin kahsewa da kuma lalata na’urorin da kamfanin ke amfani da su a filin jirgin.

Ma’aikatan filin jirgin sun ce a ranar Lahadi, kamfanin jirgin ya yi wa fasinjojin alkawarin cewa jirginsu zai tashi a ranar Litinin da karfe 10 na safe da 12 na rana, saboda matsalar da jirgin  ya samu.

“Abin takaici, sai kusan karfe 6 na yamma kamfanin jirgin saman Dana ya ba da sanarwar soke tashin jiragen biyu ba tare da wani jawabi mai gamsarwa ba, ko zaɓin maido wa jama’a kudadensu.

Dana airline yayi magana

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Litinin a shafinsa na X, hukumar gudanarwar ta nemi afuwar fasinjojin saboda jinkirin da aka samu.

Daga karshe jami’an tsaron jiragen suka shiga lamarin inda aka kira fasinjojin jiragensu suka tashi da misalin karfe 9:00 na dare.