✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau Hisbah za ta gurfanar Murja Kunya a Kotun Musulunci

Hisbah ta cika hannu da Murja Kunya kan zargin sharholiya

Hukumar Hisba ta Jihar Kano te cafke shahararriyar ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, saboda zargin ayyukan badala.

Shugaban Rundunar ‘Kai da badala’ na hukumar Aliyu Usman, ya tabbatar mana da hakan.

A cewawrsa, “Jiya (Litinin) da yamma aka kama ta a gidansu da ke unguwar Tinshama bayan kusan awa uku muna fakon ta, sannan muka yi awon gaba da ita.

“Ana zargin ta da badalda, domin akwai wanda ake zargin kullum yana zuwa ya dauke ta da misalin karfe 10 na dare, sai 12 na dare ko 1 yake dawo da ita.”

A cewarsa, za gurfanar da Murja Kunya a gaban kotun Musulunci da ke unguwar PRP a yau Talata.

Aminiya ta ruwaito cewa Hukumar Hisbah na farautar mashahuran ’yan Tiktok akalla guda shida bisa zargin yada bidiyoyi badala a shafukansu na sada zumunta, lamarin da hukumar ta ce ya saba wa dokokinta.

Wannan na zuwa ne watanni kadan bayan babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya gayyaci mata ’yan Tikto da ke Kano zuwa wani zama inda hukumar ta yi musu tayin tallafin  sana’o’i da na karatu.

A lokacin zaman taron, Sheikh Daurawa ya hori ’yan Tiktok da sauran kafafen sadarwa na zamani da su daina yada abubuwan da za su iya lalata tarbiyya.