✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasinjoji sun ƙone ƙurmus a haɗarin mota a Kogi

Haɗarin ya afku ne a gaban Kwalejin Koyarwa ta Aloma, inda duk waɗanda lamarin ya rutsa da su sun ƙone ƙurmus.

Wasu fasinjoji sun ƙone ƙurmus a safiyar wannan Lahadin a dalilin wani mummunan haɗari da ya afku a  garin Aloma da ke Ƙaramar Hukumar Ofu a Jihar Kogi.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa haɗarin wanda ya afku a gaban Kwalejin Koyarwa ta Aloma, inda ya rutsa da motocin bas guda biyu da wata motar tirela.

Majiyar ta ce, wata motar bas ƙirar Siena ce cike da fasinjoji ta yi karo da wata motar Toyota da ketahowa a ƙoƙarin kaucewa ramuka da ke kan titin kuma nan take ta kama wuta, lamarin da ya sa dukkan fasinjojin da ke cikin motar suka ƙone.

“Dukkan fasinjojin da ke cikin motar Toyota, ciki har da direban sun ƙone ƙurmus.

“Waɗanda ke cikin motar sienna su ma sun ƙone, babu wanda ya tsira.

“Wata mota da aka ajiye a kusa da wurin da lamarin ya faru ita ma ta kama wuta a yayin da lamarin ya faru kuma ta ƙone ƙurmus.

“Gobarar da ta kama motocin ta kuma lalata wani gida da ke kusa da wurin da wutar ta tashi.

“Har yanzu ba mu tabbatar da wani wanda ya tsira da ransa ba a duk cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su,” in ji Adejo Usman, wani mazaunin Aloma.

Ya ce mutanen ƙauyen ba su iya yin komai don ceto wasu fasinjojin da suka maƙale saboda babu kayan ceton gaggawa da za a iya kuɓutar da su.

Kwamandan sashin hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC), Samuel Ayedeji, ya ce yana cikin wani taro lokacin da aka tuntuɓe shi kan lamarin.