✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haɗarin mota ya laƙume rayuka 11 a Kano

An samu ƙwacewar abin hawa da ya janyo karo a tsakanin motocin biyu inda wuta nan take ta kama.

Aƙalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 16 suka samu raunuka, da kuma ceto mutum ɗaya a wani haɗarin mota da ya afku a mahaɗar Gaya da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa FRSC reshen Jihar Kano, Ibrahim Sallau-Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Labaran ya fitar ranar Asabar.

Ya ce, haɗarin ya rutsa da motoci guda biyu – wata mota ƙirar bas Toyota Hummer mai lamba KTG 190 XB da kuma ƙaramar motar Hijet mai lamba KTG 501 YG.

“Mun samu kiran waya da misalin ƙarfe 03:45 na rana a ranar 19 ga Afrilu, 2024. Da samun labarin, sai muka aika da jami’anmu da motar mu cikin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceto waɗanda abin ya shafa da ƙarfe 03:55 na rana,” a cewar Abdullahi.

Kwamandan sashin ya ce, haɗarin ya afku ne sakamakon gudun wuce gona da kima da kuma ƙwacewar abin hawa, lamarin da ya kai ga yin karo a tsakanin motocin guda biyu inda wuta nan take ta kama.

“Hatsarin ya rutsa da jimillar fasinjoji 28 a cikin motocin biyu, daga cikinsu 11 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 16 suka samu munanan raunuka, kuma an ceto ɗaya daga cikinsu.

“An kai waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Gaya domin samun kulawar gaggawa, yayin da tuni an yi jana’izar wadanda suka riga mu gidan gaskiya,” in ji Abdullahi.

Kwamandan hukuma kiyaye haduran ya jaddada mahimmancin bin dokoki da ƙa’idojin hanyoyin.