✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar tankar mai ta yi ajalin mutum 5 a Adamawa

Sama da ababen hawa 50 sun kone kurmus.

Mutum biyar sun mutu sakamakon kamawa da wuta da wata tankar man fetur ta yi a Arewacin garin Mubi da ke Jihar Adamawa.

Wani da ya gane wa idonsa, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba, yayin da wata tankar mai take juye mai cikin wasu manyan duron mai a Kasuwar Gyela.

Garin Mubi ya yi kaurin suna inda ’yan bunburutu ke yin fasa kaurin mai zuwa kasar Kamaru a cikin dare.

Wani mazaunin yankin mai suna Habu Garba, ya shaida wa Aminiya cewa akalla mutum biyar ne suka mutum sannan da dama sun ji rauni yayin da tankar ta kama da wuta.

Wani ma’aikacin agaji, Adamu Madobi, ya ce sun halarci jana’izar wasu mutum uku ’yan uwan juna da suka mutu a sakamakon lamarin.

Madobi, ya kara cewar akalla ababen 50 da ke ajiye a kusa da gidan man sun kone kurmus.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (ADDEMA), Dokta Muhammad Sulaiman, ya sanar da cewar mutum uku sun rasu yayin da wasu biyu ke karbar kulawa a asibiti.