✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Fashewar tankar mai ta hallaka mutum 6 da kone gini 30 a Kwara

An bayyana cewa motar ta kwace ne inda ta fada cikin wasu gine-gine nan take kuma ta yi bindiga.

Akalla mutum shida ne suka mutu, gine-gine 30 kuma suka kone bayan wata tankar mai ta yi bindiga a yankin Jebba da ke Karamar Hukumar Moro a Jihar Kwara.

An motar ta kwace ne inda ta fada cikin wasu gine-gine nan take kuma ta yi bindiga sakamkon man da ke tsiyaya.

Wani ganau ya ce a tarwatsewar da motar ta hallaka mutum shi, gidaje 30 tare da shaguna kuma sun kone.

Daga bisani jami’an kashe gobara na jihar sun isa wurin suka kuma kashe wutar, bayan kone wadancan gidaje da shaguna da ta yi.

Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ta hannun Sakataren Yada Labaransa, ya jajanta wa iyalai da wanda iftila’in ya shafa.

Gwamnan ya ce abun takaici ne musamman rasa rayukan mutane da aka yi a hatsarin.

Ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar SEMA, ta je wajen domin tantance yawan asarar da aka yi.