Masu kada kuri’a da ma’aikatan zabe sun ranta a na kare bayan da fashewar wani sinadari ta haddasa tarwatsa wata rumfar zabe da ke Karamar Hukumar Aba ta Arewa a jihar Abiya.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a wata rumfar zabe da ke Mazaba ta takwas dake Tsaunin Agbor a garin na Aba, a daidai lokacin da ake tsaka da zaben cike gurbi ranar Asabar
- Zamfara ta lashe Gasar Al-Kur’ani ta Kasa
- An ci tarar kamfanoni N1m saboda karya dokar tsaftar muhalli
Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ce dai take gudanar da zaben cike gurbi a Mazabar dan Majalisar Tarayya ta Aba ta Kudu da Aba ta Arewa a jihar.
Ana gudanar da zaben ne bayan mutuwar dan majalisar dake wakiltar mazabar, Hon. Ossy Prestige ranar shida ga watan Fabrairun 2021.
Kafin zaben dai, manyan ’yan siyasar yankin sun yi ta zafafan muhawarori tare da zargin junansu da yunkurin tayar da zaune tsaye lokacin zaben.
Zaben dai na gudana cikin lumana a rumfar zaben har zuwa lokacin da sinadarin wanda ake kyautata zaton bam ne ya fashe.
Aminiya ta gano cewa ba a sami asarar rai ko daya ba sanadiyyar fashewar, ko da yake wasu daga cikin kayan zabe sun lalace.
Ba a dai kai ga tantance ko an dasa bam din ne domin a razana masu zabe a rumfar zaben ba, kuma tuni jami’an tsaro suka yi wa wajen kawanya daga bisani domin dawo da doka da oda.