Wasu jami’an tsaron sa-kai biyu sun riga gidan gaskiya yayin da wasu takwas suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a Karamar Hukumar Mafa da ke Jihar Borno.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da jami’an sa-kan ke gudanar da sintiri a tsakanin garin Mafa da Konduga a ranar Talata.
- Yadda saran maciji ya kwantar da mutum 2,700 a Gombe
- Shirin Ilimantar da Matasa zai magance matsalar tsaro — Tinubu
Wakilinmu ya ruwaito cewa, a yayin sintirin ne jami’an tsaron suka taka wata nakiya da ake zargi mayakan Boko Haram sun binne a kan hanya.
Bayanai sun ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri
Haka kuma, a Yammacin Talatar ne aka yi jana’izar jami’an biyu da suka riga mu gidan gaskiya kamar yadda addinin Islama ya tanada.
Shugaban Karamar Hukumar Mafa, Honarabul Goni Gonibe wanda ya halarci jana’izar ya jajanta wa iyalan wadanda suka riga mu gidan gaskiya tare da addu’ar Allah Ya jikansu da Rahama.
Sauran wadanda suka halarci jana’izar sun haɗa da dan Majalisar Dokokin Jihar Borno mai wakiltar Mafa, Hon Baba Ali Modu da Sakataren Karamar Hukumar Mafa, Alhaji Sale Bukar, da Kwamandan rundunar sa-kai ta CJTF a Mafa da sauran al’umma.