✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda saran maciji ya kwantar da mutum 2,700 a Gombe

Likitoci sun ce mutum 30 sun mutu.

Asibitin Jinyar Cizon Maciji da ke garin Kaltungo shi ne asibiti daya tilo da jihohi 12 a fadin Najeriya ke kawo jinyar wadanda maciji ya sara.

A yanzu dai asibitin ya bunkasa inda ya zama cibiyar nazarin allurai da rigakafin saran maciji da kwarraru ke zuwa daga ciki da wajen jihar domin gudanar da nazari da bincike.

Alkalumma sun nuna cewa ana samun karuwar matsalar harbin macizai da kan rutsa da akalla mutane 500 a cikin duk mutum dubu daya na Nijeriya a duk shekara.

Jihojin Gombe, Bauchi, Borno, Nassarawa, Taraba, Kebbi, Benuwe da Oyo ne a kan gaba wajen fuskantar matsalar harbin maciji a kasar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jihohin da suke zuwa don jinya a Cibiyar Nazari da Binciken Rigakafin Saran Maciji da ke Kaltugon Gombe, sun hada da da Bauchi da Benuwe da Taraba da Nasarawa da Kogi da Borno.

Sauran jihohin sun haɗa da Enugu da Kebbi da Oyo da Adamawa da kuma Birnin Tarayya Abuja.

Dokta Niclos Ammani Hamman, wanda shi ne Babban Likitan Asibitin, ya ce a kullum suna karbar sabbin majinyata wadanda maciji ya saran akalla mutum 7 zuwa 8 daga wadannan jihohin.

A cewar Dokta Ammani, a shekarar da ta gabata sun samu majinyata sama da dubu 2,700, wanda a cikinsu su guda 30 ne kacal suka mutu.

A cewarsa, jinkirin kawo majinyatan asibitin ne ya sanya aka samu wannan adadi na wadanda rai ya yi musu halinsa.

Ya bayyana takaicin cewa galibin wadanda suke jinkirin zuwa asibitin sukan nemi magungunan gargajiya a gida, wanda sai abin ya faskara sannan a taho asibiti kuma galibi akan yi hakan ne idan lokaci ya ƙure.

Ya yi bayanin cewa an fi samun saran macijin ne a lokutan sharar gona ko kuma lokacin girbi yayin da ganye ya yi yawa da macizai suke likimo a ciyayi.

Dokta Ammani Hamman, ya ba da shawarar da zarar maciji ya sari mutum a gaggauta zuwa asibiti kuma kar a daure wajen saboda daurewar ba za ta taimaka ba.

A nasa bangaren, Kwamishinan Lafiya na Jihar Gombe, Dokta Habu Dahiru, cewa ya yi ganin asibitin ya zama cibiyar nazarin allurar saran macizai ya sa likitoci da dama daga jami’o’i suna zuwa domin gudanar da nazari.

Kwamishinan ya ce ya taba ziyartar Ministan Lafiya domin neman haɗin kai wajen ganin an sake kawo kayayyakin aiki asibitin.

Wasu majinyata da suke kwance a asibitin, Umar Ahmed daga Jihar Bauchi da Shehu Shagari daga Taraba, sun bayyana jin dadinsu kan yadda ake kula da su yayin da suke jinya a asibitin.

Sun kuma jinjina wa Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya kan yadda suke kokari wajen ganin asibitin ya fara samar da allurar saran macizan da a kullum ake nazari da bincike a kai.