✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin Ilimantar da Matasa zai magance matsalar tsaro — Tinubu

Ana ci gaba da samun karuwar satar mutane don neman kudin fansa da ke barazana a kasar.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara gagarumin shirin ilimantar da matasa a matsayin daya daga cikin hanyoyin magance matsalar tsaro.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar musuluncin nan ta Jam’iyyatu Ansaridden da ta kai ziyara Fadar Gwamnatin Najeriya ranar Talata a Abuja.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da samun karuwar satar mutane don neman kudin fansa da ke barazana ga babban birnin kasar tare da wasu yankunan Arewa da ke fama da rikici.

Tinubu ya yi Allah-wadai da sace-sacen da aka yi a matsayin “mummunan al’amari mai tayar da hankali, da kuma mugunta.”

Ya kuma bayyana samar da ilimi a matsayin “maganin matsalolin da ke ta da hankalin al’ummar kasar,” a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale.

”Babu wani makami da zai yaki talauci da ya kai karfin karatu,” in ji sanarwar.

“Hukumomin tsaro suna aiki tare da tura dakaru don magance kalubalen da ake fuskanta nan da nan, yayin da kuma za a samar da dukkan abubuwan da ake buƙata, da manufofi da tsare-tsare nan ba da jimawa ba don ilimantar da matasan Najeriya.”

Tuni dai jami’an tsaron Najeriya ke fafatawa da ’yan tawayen da ke tayar da kayar baya a yankin Arewa maso gabas baya ga kungiyoyin da ke dauke da makamai wadanda galibi ke aiwatar da kashe-kashe da sace-sace a wasu al’ummomin yankunan karkara a Arewa maso Yamma da tsakiyar kasar.

Ana iya tuna cewa, Shugaba Tinubu bayan lashe zaben shekarar da ta gabata, ya yi alkawarin kawar da matsalar rashin tsaro a kasar.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da kai munanan hare-hare musamman a arewacin kasar, inda babban birnin tarayya Abuja ke samun karuwar sace-sacen mutane a manyan tituna da kuma gidaje a ’yan makwannin nan.

Yanzu haka mazauna wajen Abuja sun fara yin kaura a daidai lokacin da ake samun yawaitar sace-sacen mutane don neman kudin fansa da ake zargin ’yan bindiga ne daga jihohin da ke makwabtaka da birnin.