Farfesa Nora Daduut ta jam’iyyar APC ce ta lashe zaben cike gurbi kujerar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Filato ta Kudu da aka gudanar a ranar Asabar.
Sakamakon zaben cike gurbin da Hukumar Zave ta Kasa (INEC), ta bayyana ya nuna cewa Farfesa Nora Daduut ta lashe zaben da kuri’a 83,15104 a yayin da George Daika na jam’iyyar PDP da suka fafata ya samu kuri’a 70,838.
- ‘Dalilin da muke zawarcin Tambuwal ya fito takara a 2023’
- Zaben cike gurbin Majalisar Dokokin Zamfara bai kammala ba – INEC
Har’ila yau sakamakon zaben, ya nuna cewa Farfesa Nora ta kayar da George Daika, a kananan hukumomi hudu da mazabar ta kunsa, shi kuma ya samu kananan hukumomi biyu.
Da yake jawabi kan sakamakon zaben, Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya taya Farfesa Nora murnar nasarar da ta samu na lashe zaben.
Ya ce babu shakka wannan nasara da jam’iyyar APC ta samu ya nuna cewa jam’iyyar ta dasa saiwoyinta a duk lungu da sako na jihar.
Ya yi kira ga wadanda suka yi wannan takara, su zo a hada kai domin a ciyar da mazara da jihar baki daya gaba.